Wani mutumi ya kusa kashe diyar sa saboda Amalala
– Wani mutumi mai suna Benjamin Endurance ya kona diyar cikin sa da ruwan zafi saboda tana yawan amalala
– Wannan abu ya faru ne a Bayelsa, Yarinyar ba ta wuce shekaru hudu ba a duniya
– Yanzu haka an garzaya da Mista Benjamin Kotu
Wani mutumi mai suna Benjamin Endurance dan Jihar Bayelsa ya kona diyar cikin sa da ya haifa da ruwan zafi saboda tana yawan fitsarin kwance watau amalala. A makon jiya ne dai aka yi Kotu da Mista Benjamin a Birnin Yenagoa Inji Jaridar Dailypost.
An bayyana cewa Mista Benjamin Endurance tare da matar sa, kuma kishiyar wannan karamar yarinya suna azabtar da wannan karamar yarinya mai shekaru hudu a duniya ne saboda kawai tana amalala.
KU KARANTA: An kama ta da Koken a rigar mama
Kakakin ‘Yan Sanda na Garin Okaka, da ke Birnin Yenagoa wanda shine Babban Birnin Bayelsa, Asinim Butswat ya tabbatar da cewa Mahaifin wannan diya mai shekaru 36 a duniya ya kona yarinyar da ruwan zafi, inda ta samu ciwo na kuna sosai. An samu cewa makwabta ne suka kai karar abin da ya ke faruwa.
Yanzu dai Kungiyar Lauyoyin mata na duniya sun kai wannan uba Kotu Majistare da ke Garin, ana zargin sa da Konawa diyar sa kafafu da tafasshen ruwan zafi saboda fitsarin kwance watau amalala. Ana zargin sa da laifuffuka guda uku; ciki har da rashin ba yarinyar magani da kuma kokarin hana zaman lafiya. Alkali mai shari’a ta dage zaman bayan da uban yace bai da laifi.
Asali: Legit.ng