Abubuwa 10 da suka sa Emmanuel Adebayor ya musulunta

Abubuwa 10 da suka sa Emmanuel Adebayor ya musulunta

- Dan wasan kwallon kafar nan, Emmanuel Adebayor ya bayyana abin da ya sa ya shiga Addinin musulunci

- Emmanuel Adebayor yace ya gane cewa Musulunci shine addinin gaskiya ko a cikin littafin bible

- Fitaccen dan kwallon yace ya fahimci cewa Musulmai sune asalin mabiya Yesu Almasihu

Abubuwa 10 da suka sa Emmanuel Adebayor ya musulunta
Emmanuel Adebayor

 

 

 

 

 

 

 

A kwanakin baya can, an bayyana cewa Fitaccen dan wasan kwallon Kafar nan Emmanuel Adebayor ya bar addinin Kirista, Emmanuel Adebayor ya musulunta, ya kuma bayyana dalilan da suka sa ya shiga wannan addini na Islama. Emmanuel Adebayor yace ya gane cewa Musulmai ne asalin mabiya Yesu Almasihu AS.

KU KARANTA: Shekaru goma da nada Sarkin musulmi

1. Tsohon dan kwallon na Arsenal yace Littafin Bible ya tabbatar da cewa Ubangiji daya ne a Surar Mark ta 12 Aya ta 29 da wasu wuraren, Musulmai ma suna bautar Allah daya (4: 171)

2. Yesu AS ya haramta cin Alade a Surar Leviticus a Aya ta 7, haka Islama ya haramta a Sura ta 6: 145.

3. Yesu AS ya kan ce Idan Allah ya yarda, haka Musulmai na cewa In shaa Allah. (Sura ta 18: 23-24) kafin suyi kowane irin abu.

4. Kuma Yesu AS na yin Sallama ga mutane kamar yadda musulmai ke cewa Amincin Allah a gare ku watau Salam Alaikum. (John 20: 21)

5. Bible ya koyar da wanke fuska da hannuwa kafin ayi Sallah, kamar dai yadda musulmai ke alwala ko taimama.

6. Hatta Sallar ma da musulmai ke yi, haka ya zo a Littafin bible (Mathew 26: 39) ake sallah, watau a fadi da kai ayi Sujuda.

7. Yesu AS na barin gemu kamar yadda Musulunci ya koyar, haka ita kuma Mahaifiyar sa Nana Maryama AS tana lullube jikin ta, kamar dai yadda ya tabbata a cikin Genesis , Timothy da Corinthians da kuma Qur’an 33:59.

8. Yesu AS na yin azumi na kwanaki kusan 40 a jere (Exodus 34: 28) dsr, Musulmai kan yi azumin Ramadana su kuma daura da wasu kari bayan nan.

9. An yi wa Yesu AS kaciya lokacin yana kwana takwas a duniya (Luke 2: 21), kamar yadda aka yi wa Annabi Muhammadu SAW (Sahih Bukhari, Muslim da Ahmad)

10. Yesu AS da kan say a kira Ubangiji da suna ‘Elah’ watau kamar dai ‘Allah’da larabci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng