Ka daina sa jar hula koko mu kai ka kara- An gaya ma Ganduje

Ka daina sa jar hula koko mu kai ka kara- An gaya ma Ganduje

 - Gungun wasu masu ra'ayin Kwankwasiyya sun ba gwamna Ganduje awa 48 ya rabu da jar hularsa wadda tsohon gwamna Kwankwaso  ya kirkiro a 2011

- Gungun sunce zasu kai Ganduje kara in bai bar sanya jar hular ba

- Masu ra'ayin Kwankwasiyyar sun nemi gafarar Kanawa domin kawo masu Ganduje a matsayin gwamna

Ka daina sa jar hula koko mu kai ka kara- An gaya ma Ganduje
Gwamna Ganduje da kwankwaso

Wani gungun masu sa ido kan siyasa a jihar Kano kalkashin sunan masu ra'ayin Kwankwasiyya sun baiwa gwamna Abdullahi Ganduje awowi 48 daya daina sa jar hula koko su kai kararsa, This Day ta ruwaito. A cewar gungun, tunda Ganduje baya tare dasu, shi da magoya bayansa ya kamata su daina sanya "jar hula" wadda ke da alaka da Kwankwaso yayin mulkinsa na gwamnan jihar Kano.

KU KARANTA: An kusa fara bikin cika shekaru goma da hawan Sarkin Musulmi

Yayin da yake magana da 'yan jarida ranar Juma'a 21 ga Oktoba wajen bikin cika shekaru 6 da kirkiro gungun, da kuma cika shekaru 60 da haifuwar wanda ya kirkiro ta, sanata Rabi'u Kwankwaso, shugaban Hannun Karba,'Alhaji Sharu Garba Gwammaja, yace Ganduje yaci amanar gungun

Asali: Legit.ng

Online view pixel