Shekaru 10 da nada Sultan Sa’ad Abubakar Sarkin Musulmi

Shekaru 10 da nada Sultan Sa’ad Abubakar Sarkin Musulmi

Gwamnatin Jihar Sokoto za ta yi bikin cika Shekara goma da nada Alhaji Sa’ad Abubakar Sarkin Musulmi

Za a kaddamar da littafi na Mai girma Sultan Sa’ad Abubakar a wannan rana

An nada Mai girma Sa’ad Abubakar III Sarkin Musulmi bayan rasuwar Muhammadu Maccido

Shekaru 10 da nada Sultan Sa’ad Abubakar Sarkin Musulmi

A cikin watan Nuwamban nan mai zuwa ne za a cika shekaru goma daidai da nada Mai Girma Alhaji Sa’ad Abubakar III a matsayin Sultan na Sokoto, watau Sarkin Musulmi. Kwamishinan labarai na Jihar Sokoto, Danladi Bako ya bayyana haka a yau, Inji Jaridar DailyTrust.

Za a gudanar da wani taro na Ilmi a ranar cika shekara goma na Sarkin, inda za a kaddamar da wani littafi game da rayuwar Sarakun Musulmi. Littafin zai yi magana ne game da gudumuwar Sarakunan Musulmai wajen tattalin arzikin Kasa da kuma Siyasar al’umma da mulki a yankin na Sahel.

KU KARANTA: Ana bukatar juyin juya hali a Najeriya

Kwamishinan labarai na Jihar Sokoto, Danladi Bako wanda shine ke rike da Sarautar Kogunan Sokoto, kuma yana cikin wadanda za su gudanar da wannan taro, yace za ayi taron ne a Ranar 2 ga watan Nuwamban gobe. Bako yace za a gayyaci manyan masana na duniya zuwa wannan taro.

Alhaji Danladi Bako yace za a duba binciken su Shehu Danfodio da kuma dan sa Abdullahi na Gwandu dsr, yace a bakin na Sarkin Musulmi za kuma ayi hawan Durbar. An nada Mai Girma Alhaji Sa’ad Abubakar III a matsayin Sultan na Sokoto, watau Sarkin Musulmi a shekarar 2006.

Asali: Legit.ng

Online view pixel