Sanata Binta masi tayi barkwanci a Majalisa

Sanata Binta masi tayi barkwanci a Majalisa

- Sanata Binta Masi Garba tace abunda ya fi komai mahimmanci gareta kafin zama sanata shine kicin.                                                              

- Tayi raha da cewa kancewa da daya dakin.

Dan gane da martani da Buhari ya mai da ma matarshi da yace matar ta kasance a kicin din shi, ya cigaba da kawo cece kuce a tsakanin mutanen kasar nan.

Wannan lokacin sanata Binta Masi Garba, wadda ke wakiltar Adamawa ta arewa karkashin jam'iyyar APC, ita ce daya daga cikin mutanen da suka tsoma albarkacin bakin su.

Sanata Binta masi tayi barkwanci a Majalisa
Sanata Binta Masi Garba

Sanata Binta Masi tace kafin ta zama sanata babban abunda yake da mahimmanci gareta kafin zama sanata shine kasance warta a kicin.

Sai dai martanin da shugaban kasa Muhammad Buhari yayi yasa manyan mata da rashin jin dadi, Sanata Binta tayi raha da yadda da cewa mahimmancinta ya fara a kicin kuma ze kare a kicin.

Kamar yadda ta bayyana a taron sanatoci ranar laraba 19 ga watan Oktoba, tace abunda ya fi komai mahimmanci gareta kafin zama sanata shine kasance warta a kicin.

KU KARANTA KUMA: Yadda yaran masu kudi ke jin dadi

"Ina alfaharin kasance wa a kicin da daya dakin. Kafin in zama sanata abunda yake da mahimmanci shine kasancewa ta a kicin".

Sai gurin ya kaure da dariya.

Da ta cigaba da magana kuma, sanata ta kalubalanci yan Najeriya da suyi duba da irin tashin hankalin da yan matan chibok da aka saki kwanan suka shiga kuma tayi kira ga masu duba yana yin dan adam su taimaka dan sun manta da abubuwan da suka shiga lokacin da suke a kame.

In zaku iya tunawa a makon da ta gabata shugaba Buhari ya mai da martani kan firar da akayi da matar sa a BBC in da tayi ikirarin cewa Kila ba zata goya ma mijin ta baya ba har sai ya canza yadda ya bada makaman sa da ta nada.

Inda ya mai da mata da martani a lokacin yana kasar Jamus inda ya kai ziyarar kwana ki 3 kan matsalar tsaro da tattalin arziki inda yayi dariya yace" mata ta ta mallakin kicin dita ce da dakin zama da daya dakin".

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng