Wasu yan matan Chibok sun fi son zama a dajin Sambisa

Wasu yan matan Chibok sun fi son zama a dajin Sambisa

- Wasu rahotannin na cewa fiye da 'yan matan Chibok 100 daya da ke hannun 'yan Boko Haram sun fi son zama a hannun mayakan maimakon dawowa wurin iyayensu.

- Shugaban kungiyar cigaban al'ummar Chibok, Mr Pogba Bitrus, wanda ya bayyana hakan ga kamfanin dillancin labarai na AP, ya ce yana ganin 'yan Boko Haram sun sauya tunanin 'ya'yan nasu ne.

Wasu yan matan Chibok sun fi son zama a dajin Sambisa
Shugaba Buhari, mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi tare da yan matan chibok da aka saka

Ko kuma a cewarsa, 'yan matan suna jin kunyar dawowa gida saboda gudun yadda jama'a za su rika kallonsu, ko kuma su fuskanci tsangwama.

Rahotannin sun bayyana ne a yayin da shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya sha alwashin kara zage damtse wajen ganin an sako karin 'yan matan 83.

KU KARANTA KUMA: Matsin tattalin arziki a ya shafi Wasu jiragen kasashen waje

A makon da ya gabata ne bisa wata yarjejeniya da kungiyar agaji ta Red Cross da gwamnatin Switzerland suka shiga tsakani, aka sako 21 daga cikin 'yan matan bayan shafe fiye da shekara biyu.

A watan Afrilun 2014 ne dai Boko Haram ta sace 'yan matan sama da 200, a makarantarsu da ke garin Chibok, na jihar Borno, a lokacin da suke jarrabawa, lamarin da ya ja hankalin duniya.

Kuma a ranar Lahadi ne suka gana da iyayensu cikin annashuwa, a karon farko tun bayan sace su.

Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari, ya gana da 'yan matan Chibok 21 da mayakan Boko Haram suka sako, bayan shafe fiye da shekara biyu a hannunsu.

A ranar Alhamis ne aka sako 'yan matan sakamakon yarjejeniyar da aka cimma da mayakan, wacce kungiyar Red Cross da kasar Switzerland suka shiga tsakani.

KU KARANTA KUMA: Kungiyar iyayen matan Chibok sun fitar da wata sanarwa

Shugaba Buhari ya ce "Sun ga dukkan wani abu mai muni da dan adam zai iya gani a duniya. Yanzu lokaci ya yi da za su hadu da abin alheri".

Ya kara da cewa, gwamnati za ta kula da lafiyarsu, da inganta rayuwarsu sannan kuma ta tallafa musu.

"Gwamnatin tarayya za ta sauya rayuwarsu, sannan ta tabbata cewa sun koma sun ci gaba da rayuwa cikin al'umma ba tare da bata lokaci ba".

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng