Wata katuwar macijiya tayi kokarin cin kada

Wata katuwar macijiya tayi kokarin cin kada

 Manyan macizai sun cika hadama, kuma su macizaine masu hadari, suna cin duk wata halitta kome hadarin ta, amma me kuke ze faru in maciji yaje gurin abunda yafi karfin sa.

Wannan macijin ya zama babba a cikin sauran manyan macizai, eh zaka iya samun wanda yafi wannan girma, amma dai wannan ya kai tsawon mita 4, irin wannan halittar ze iya hadiye mutum a take, sai dai anyi sa'a ba wani dan adam da yake gurin a lokacin da yake jin yunwa.

Wata katuwar macijiya tayi kokarin cin kada

Sai dai ya fada ma kada, sai dai abin tausayi ba wanda yaga abunda ya faru, amma dai macijiyar ta cinye kadan, kuma ya hadiye kadan a lokaci daya, daga baya wasu masu jirgin ruwa sunzo wucewa, sai su ka ga abun tashin hankalin.

KU KARANTA KUMA: Wata malama tayi lalata da dalibai

Sai ga katuwar macijiya ta rabe biyu, gawar kadar koma a gefen cikin ta, masu ilimin kimiyya sunce, da macijin ta hada kadan ta kasa narkar da shi a cikin ta, shine dalilin fashewar macijin.

Wannan abun mamaki ne matuka, shiyasa ake cewa kar kaci abunda baka iya taunawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng