Aisha Buhari sanye da rigar naira miliyan 1.2

Aisha Buhari sanye da rigar naira miliyan 1.2

A jiya Talata 18 ga watan Oktoba ne Uwargidar shugaban kasa Muhammadu Buhari, Aisha Buhari ta kama hanyar zuwa kasar Beljam sanye da rigan N1.2m don halartan taron mata.

Aisha Buhari sanye da rigar naira miliyan 1.2
Uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari

A yanzu haka Aisha ta sauka garin Brussel, Beljam don halartan wani taron mata inda ake sa ran zata karanta kasida ma taken “rawar da mata ya kamata su taka wajen kawo zaman lafiya a duniya”, sai dai ba kamar yadda aka saba a baya ba, jirgin kasa Aisha Buhari tabi zuwa Brussel ba jirgin sama ba.

Sai dai yan Najeriya da dama sun caccaki uwargidan shugaban kasan saboda sanya wannan riga mai tsada mai suna SALVATORE FERRGAMO, yayin da yan gudun hijira a Najeriya suke fama da yunwa.

Aisha Buhari sanye da rigar naira miliyan 1.2

KU KARANTA: Ma’aurata sun haifi yan-biyu biyu a shekaru biyu

Dayake dai dama Aisha Buhari ta saba shan suka game da adonta, idan ba’a manta ba, an hangi Aisha sanye da agogon naira miliyan 10 a ranar da aka rantsar da shugaba Buhari, amma daga bisani bincike daga kamfanin agogon ya bayyana cewa farashin agogon bai kai naira 100,000 ba.

Sa’annan kimanin wata guda kenan, da aka hange ta a kasar Amurka rike da jakan Hermes Birkin 35cm Porosus Crocodile Bag, masana kayan ado sunce, indai jakan nata ba jabu bane, toh tabbasa farashinsa ya kai naira miliyan 34.

Aisha Buhari sanye da rigar naira miliyan 1.2

zuwa yanzu dai yan Najeriya suna ta cecekuce kan batun.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel