Muhimman labaran ranan talata

Muhimman labaran ranan talata

Jaridar NAIJ.con tattaro muku muhimman labaran ranan talata 19 ga watan oktoba 2016

1.'Yan Najeriya na fadin ra'ayinsu kan kama matar Femi Fanj-Kayode da dansu

Muhimman labaran ranan talata
Hukumar EFCC ta tsare matar Femi Fani-Kayode da dansu

Hukumar hana almundahana da yima tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta tsare matar Femi Fani- Kayode, tsohon ministan sufurin jiragen sama ranar Litinin 17 ga Oktoba a garin Ado Ekiti. A cewar mista Kayode kamar yadda ya nuna fushinsa na Facebook inda yake cewa an tsare matarsa Precious Chikwendu da yaronsu dan wata 8 Aragorn, kuma an muzguna masu.

2. A Kaduna: 3 sun mutu an kuma sace shanu 100 yayin da 'yan bindiga ke barna

Muhimman labaran ranan talata
Yan zanga-zanga

A kalla mutane ukku sun rasa rayukansu bayan harin da wasu 'Yan Bindiga da ake zaton Fulani makiyaya ne suka kai daren Lahadi 16 ga Oktoba, suka mamaye unguwar Galwyi dake cikin karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna, cewar jaridar The Punch.

3.EFCC tayi Magana akan yunkurin tsare uwargidan Fani-Kayode

Muhimman labaran ranan talata

Tsohon ministan sifurin jirgin sama , Femi Fani-Kayode, ta tuhumci jami’an hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC da damke uwargidansa Precious Chikwendu da dan jaririnsa a ranan liinin 17 ga watan oktoba.

Amma kakakin hukumar Wilson Uwujaren,ya musanta maganar saboda hukumar batada jami’a a jihar Ekiti.

4. Shin mai ya faru da kudaden da EFCC ta karba ne?

Muhimman labaran ranan talata
Kudaden da hukumar EFCC ta kwato

Hukumar hana almundahana da yima tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC tace ta amshi makudan kudi domin farfado da tattalin arzikin kasa har sai idan kotu ta bayar da izini.

5. Darajar naira ta karu zuwa N455/$1 a Kasuwar shinku

Muhimman labaran ranan talata

Ranar Litinin 17 ga Oktoba, darajar naira ta kara yin sama a kasuwar bayan fage inda aka rufe kasuwar tana N455/$1. Wannan ya zama sama ga N460/&1 da take a ranar Juma'a 14 ga Oktoba

6. Fadar shugaban kasa tayi magana kan sakin 'yan matan Chibok da shirinta na gaba

Muhimman labaran ranan talata
Mista Femi Adesina,

Daga Edita: Femi Adesina, mai baiwa shugaba Muhammadu Buhari shawara kan kafofin sadarwa da watsa labarai ya bakunci Channels Television inda yayi magana kan sakin 'yan matan Chibom 21 da aka sace, da kuma kokarin da gwamnatin tarayya keyi na tabbatar da an sako sauran yaran dake tsare.

Asali: Legit.ng

Online view pixel