Fadar shugaban kasa tayi magana kan shirinta na gaba
Daga Edita: Femi Adesina, mai baiwa shugaba Muhammadu Buhari shawara kan kafofin sadarwa da watsa labarai ya bakunci Channels Television inda yayi magana kan sakin 'yan matan Chibok 21 da aka sace, da kuma kokarin da gwamnatin tarayya keyi na tabbatar da an sako sauran yaran dake tsare.
Temidayo Akinsuyi, ya kalli hirar, kuma ya gutsuro wasu daga cikin abinda suka tattauna
Tambaya: Ya Kaji game da sakin 21 daga cikin yaran da aka sace?
Amsa: Ina mai matukar farin ciki, ina taya bil'adama da 'yan Najeriya da mutanen Chibok, 'yan matan, iyayensu da kuma kowa da kowa murna. Wannan rana ce mai kyawo.
Tambaya: Shin wannan saki ne koko kubutarwa?
Amsa: Saki ne. Akwai banbanci tsakanin saki da kubutarwa. Saki ne bayan tattaunawa kamar yadda ministan watsa labarai (Alhaji Lai Muhammed) yace jiya. Saki ne na kara kawo yarda tsakanin bangarorin biyu. Mataki ne wanda za'a ga irinsa nan gaba.
KU KARANTA: An bayyana babban makiyin Shugaban Kasa Buhari
Tambaya: Tabbas in muna zancen tattaunawa, dole ka bada kamar yadda zaka amsa. Me muka bada domin sakin 'yan matan nan?
Amsa: E, munji kuma mun karanta abubuwa da yawa game da abinda muka bada da wanda bamu bada ba. Tunda bamu warin, kuma harka ce ta tsaro sai mu amince da abinda jami'an tsaro suka fada, kuma abinda suka ce shine ba abinda muka bada. Cewa wannan mataki ne na amincewa. Saboda haka sai mu amince da abinda aka gaya mana
Tambaya: Zai yi wuya 'yan Najeriya su amince da haka, domin anyi tattaunawa da dama da kungiyar a baya ba tare da wata nasara ba. Na yanzu ya kawo sakamako mai kyawu. Me ya canza?
Amsa: akwai wani karin magana dake cewa: " Ga wadanda suka amince ba sai anyi wani bayani ba da wadanda ke cewa babu wani bayanin da za'a iya yi", ina bayan masu cewa babu dalilin wani bayani. Na yarda kawai, domin wannan mataki ne na amincewa. A baya anyi tattaunawar da bata ci nasara ba, kila Boko Haram bata amince da gwamnati ba, amma yanzu ta amince, kuma kada ka manta an shigo da gwamnatin wata kasa cikin tattaunawar, kila shi ya Kara jaza amincewar
Asali: Legit.ng