Mutumin nan mai mata 86 yace yana nan da rai bai mutu ba
– Bello Abubakar Masaba, mutumin da ya auri mata barkatai yace fa yana da lafiyar sa bai mutu ba
– Masaba yana da mata fiye da 80
– A ranar Asabar aka yi ta yada labarin cewa Bello Masaba ya rasu, yace ko rashin lafiya bai yi ba
Idan ba a manta Bello Abubakar Masaba, wani mutumin Bida ta Jihar Neja mai mata barkatai. A karshen makon nan ne aka yi ta yada rade-radin cewa ya mutu a Ranar Asabar din nan, aka ce wai yayi ta rashin lafiya, yayi jinya.
Sai kuwa ga shi Bello Masaba ya fito yace yana nan fa da ran sa, ya bayyana haka ne ta wayar tarho da yayi da ‘Yan jaridar Daily Trust. Masaba yace ko kwarzane bai yi ba, balle wani ciwo, ina kuma ga mutuwa? Yace yana nan cikin koshin lafiya da ran sa.
KU KARANTA: An saki wasu daga cikin matan Chibok
Masaba yace makiya ne kurum ke yada karyar mutuwar sa, sai dai yace Ubangiji ya fi su, ya kuma sa ya sha gaban su. Bello Masaba yace ‘ku zo Bida, za ku same ni, da iyali na cikin koshin lafiya…’ Masaba yace wasu marasa imani ne kurum suka yada wannan karya.
Bello Masaba dai kowa ya san sa da yawan mata, ace mai mata 86, yayi mata kusan guda 107, har yanzu kuma yana tare da kusan guda 80, bayan ya rabu da wasu da dama. Yana da ‘ya ‘ya guda 185, sai dai wasu daya sun rasu, yanzy ‘ya ‘yan na sa ba su wuce guda 133.
Asali: Legit.ng