Batun Ifiritu a Villa: Wani ya karyata su Reuben Abati

Batun Ifiritu a Villa: Wani ya karyata su Reuben Abati

Wani wanda ya taba aiki tare da Tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo ya karyata su Reuben Abati

Reuben Abati da Fani-Kayode sun ce akwai wasu bakaken ‘Ifiritu’ a cikin Fadar Aso Villa

Dr. Awosan yace watakila dai su Reuben Abati sun yi wasu miyagun abubuwa ne

Batun Ifiritu a Villa: Wani ya karyata su Reuben Abati
Dr. Sanya Awosan ya karyata su Reuben Abati

A wancan makon ne Reuben Abati yayi rubutu inda yace akwai wasu bakaken aljannu ‘Ifiritu’ da ke cikin fadar Aso Villa. Reuben Abati ne mai magana da bakin Tsohon Shugaban Kasa Jonathan Goodluck a wancan lokaci. Fani-Kayode, wanda ya taba aiki da Tsohon Shugaban Kasa Obasanjo yace kwarai haka abin yake, akwai wasu bakaken aljannu dake yawo a gidan.

Sai dai Dr. Olusanya Awosan, wanda ya rike matsayin mai bada shawara game da harkar huldodi lokacin Shugaba Jonathan yace wannan maganar, karya ce. Dr. Awosan ya tabbatar mana cewa maganar su Reuben Abati da Femi Fani-Kayode ba gaskiya bace ko kadan.

KU KARANTA: Wuta ta kona dan kwamishina yana kwance da budurwa

Dr. Olusanya Awosan yace yayi aiki da Shugabannin Kasa har biyu, yace bai taba kawowa ga wannan labari na bakaken aljanu ba. Yace watakila dai Dr. Reuben Abati da Femi Fani-Kayode sun dan taba harka ne da bakaken Aljanun a lokacin su. Olusanya Awosan yace akwai kyau su Reuben Abati su binciki kan su, amma Aso Villa fa fara ce.

Shi dai Reuben Abati yana ganin akwai wasu Ifiritu da suke sa mutum yaba abubuwa ba daidai ba da dai sauran su a cikin gidan nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel