Muhimman labaran karshen makon da ya gabata

Muhimman labaran karshen makon da ya gabata

Jaridar Legit.ng ta tattaro muku muhimman labaran da sukayi kani a waanan karshen makon da ya gabata

1. Hukumar Kwastam ta sallami hafsoshi 17

Muhimman labaran karshen makon da ya gabata
Jami'an kwastam

Hukumar Kwastam ta kasa tayi wata shara a aikinta yayinda ta kori ma’aikata 17 daga aikinsu saboda laifuka da dama,wanda ya kunshi : hulda da muggan kwayoyi, aikin jabun takardan karatu, sata, da kuma rashin zuwa aiki daga watan junairu zuwa satumban 2016.

Kakakin hukumar, Wale Adeniyi, ya bayyana cewa 2 daga cikin wadanda aka kora saboda basu son zuwa aikine amma daya dan kwaya ne.

KU KARANTA KUMA: An ga kwarangwal a gidan fasto

2. Sai na hukunta duk wanda yayi rashawa - Buhari

Muhimman labaran karshen makon da ya gabata
Shugaban kasa Muhammadu Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya alanta yakin d rashawa kuma yace sai gwamnatinsa ta hukunta duk wanda aka kama da kashi a gindi.

A yanzu haka, shugaba Buhari  na artabu ne a kungiyar lauyoyi akan damke Alkalai da hukumar DSS tayi wanda aka ce ya saba doka.

3. Justice Samson Uwaifo yace a daure Alkalai masu rashawa

Muhimman labaran karshen makon da ya gabata
Justice Samson Uwaifo

Justice Samson Uwaifo ya siffanta alkalai masu rashawa da barayi kuma yace a daure su

Alkalin kotun kolin wanda yayi ritaya yayi bayani akan wannan matsala na cewa jami’an DSS suka kai a ranan asabar, 8 ga watan oktoba. A wata hira da ya gabatar da gidan talabijin Channels, Justice Samson Uwaifo akwai alkalai masu ci da rashawa.

KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya dawo Najeriya

4. DHQ ta karyata cewa bata da masaniyar sakin 'yan matan Chibok

Muhimman labaran karshen makon da ya gabata
Leftar Janar Gabriel Olonisakin

Helkwatar rundunonin tsaro ta Najeriya ta musanta rohotanni daga wasu jaridun yanar gizo da kuma wadanda ake bugawa yau da kullum cewa bata da masaniyar sakin 'yan matan Chibok 21 da Boko Haram tayi.

5. Sakin 'yan matan Chibok: Shin Jonathan ya buya ne?

Muhimman labaran karshen makon da ya gabata
Tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan

Daga Edita: Yayin da duniya ke marhabin sakin 21 daga cikin 'yan matan Chibok da Boko Haram ta sace, Goodluck Jonathan, wanda kalkashin mulkinsa aka sace yaran bai ce uffan ba

Kess Ewubare, wani karamin Edita a Legit.ng a cikin wata kasida na ingiza Jonathan daya shiga sahun masu murna da komawar yaran gidajensu bayan ya gaza kubutar dasu a lokacin mulkinsa

6. Buhari ya ziyarci babban hafsan soja a asibitin Berlin

Muhimman labaran karshen makon da ya gabata
Shugaba Muhammadu Buhari tare da Janar MSA Aliyu

Ranar Assabat 15 ga Oktoba, shugaba Muhammadu Buhari yayi wata ziyarar ba zata ga kwamanda mai rikon gadon na runduna ta 3 ta sojojin Naneriya Birgediya Janar MSA Aliyu a wani asibiti a Berlin ta kasar Jamus. Haka. Ya faru watanni shidda bayan hafsan ya samu wani mummunan hadarin mota yayin da yake aikinsa na soja a arewa maso gabashin kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng