Wani mutum ya saki machizai 285, kawai sai wannan abun ya
Abin mamaki baya karewa, yayin da wani mutum wanda yake kama machizai wanda ake kira da Salem Khan, ya baiwa kowa mamaki sakamakon sakin machizan da yayi a dajin Indiya.
Salem Khan yana zazzage buhun machizai a dajin Indiya.
A hoton dai, anga Salem Kham yana zazzage buhun machizai a dajin Indiya, wanda bama wai zazzagewa kawai yake yiba, harma yana watsi dasu a dajin, a inda wani ya lake a jikin wandansa. Salem Khan, wanda yakai kimanin shekaru 30 yana sana'ar kama machizai yace, rana daya ne dana saki kimanin machizai guda 60 wa'anda sun kasance masu hatsarin gaske ne, wanda suka hada da Cobra a cikin su.
Salem, yana fiddo da machizai
A inda daga baya aka ganshi yana addu'a bayan ya gama sakin machizan.
Salem Khan yana ware mashizai a cikin dajin Injiya
Salem Khan yana addu'a bayan daya gama zubar da machizan.
Hmm, abin mamaki, komai Salem Khan yasa yayi haka, oho.
Asali: Legit.ng