Sakin ‘Yan Matan Chibok duk rudun banza ce-Gwamna Fayose

Sakin ‘Yan Matan Chibok duk rudun banza ce-Gwamna Fayose

Gwamna Fayose na Jihar Ekiti yace sakin ‘Yan Matan Chibok dinnan duk hanyaniyar banza ce kurum

Gwamna Fayose yace ana nema ne a kauda kawunan mutane daga matasalar tattalin arzikin Kasar da ake fama da ita

A jiya ne aka saki wasu daga cikin ‘Yan matan Chibok da aka sace fiye shekaru biyu da suka wuce a Jihar Borno

Sakin ‘Yan Matan Chibok duk rudun banza ce-Gwamna Fayose

 

 

 

Gwamnan Jihar Ekiti Ayo Fayose yace bai ga abin farin ciki ba da Gwamnatin Kasar ke yi na kubuto da ‘Yan matan Chibok da aka sace shekaru fiye da biyu da suka wuce. Gwamna Fayose yace wannan kawai kokarin kauda hankalin ‘Yan Najeriya ne daga halin da ake ciki a fadin Kasar.

Gwamna Fayose yace kubuto da wasu daga cikin ‘Yan matan Chibok ba zai canza wahalar da ‘Yan Najeriya suke sha ba a Kasar nan. Gwamnan Jihar Ekiti Ayo Fayose yace mafi damar ‘Yan Najeriya suna fama da wahala a halin yanzu.

KU KARANTA: Alkalan da aka kama sun shiga uku

Gwamnan Jihar Ekiti Ayo Fayose yace ba abin da ‘Yan Najeriya za su iya sai addu’a ko Ubangiji ya kawo saukin wannann wahala da ake fama da ita. Gwamnan Fayose yayi wannan magana ne jiya a Garin Iyin-Ekiti da ke Karamar Hukumar Ifelodun/Irepodun yayin da yake bude wasu ajijuwa. Fayose yace ba ta ‘Yan matan Chibok ake ba, yanzu yunwa ake fama da ita.

Sai dai Gwamnan Jihar Borno ya yabawa Shugaba Muhammadu Buhari da kuma Sojojin Kasar da suka taimaka wajen kubuto wasu daga cikin ‘Yan matan Chibok din, yace su mutanen Borno, babu wadanda rikicin Boko Haram ya shafa irin su.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel