Ana cacar-baki a jihar Neja tsakanin PDP da APC

Ana cacar-baki a jihar Neja tsakanin PDP da APC

Kalaman da gwamnan jihar Neja Alhaji Abubakar Sani Bello yayi akan lalacewar hanyar da ta hada Minna fadar gwamnatin jihar da kuma Abuja birnin tarayya ya hargitsa babbar jam’iyyar Adawa a jihar PDP.

Ana cacar-baki a jihar Neja tsakanin PDP da APC
Niger state governor, Abubakar Sani Bello

A ranar Talatar da ta gabata ne gwamna Alhaji Abubakar Sani Bello, ya bayyanawa manema labarai bacin ransa akan yadda yace yayi fafutukar samun kudin da ya gyara hanyar, amma yanzu ‘kasa da watanni Hudu kenan manyan motocin dakon Kaya suka lalata hanyar.

Jin kalaman gwamnan yasa jam’iyyar adawa ta PDP ta kira wani taron manema labarai, inda tace kalaman gwamnan abin mamaki ne da kuma ban al’ajabi. Mataimakin shugaban PDP mai kula da shiya ta Uku a jihar, Yahaya Abiliti, shine ya mayar da martanin inda yace abin kunya ne ace gwamnan yace yayi fafutuka wajen neman kudin da aka gyara hanyar, kuma gwamnatin tarayya ce ta biya kudin.

Sai dai kakakin gwamnan jihar Nejan Jibril Baba, yace wadannan kalamai ne kawai irin na siyasa ya kuma kara da cewa duk wanda yake ‘dan jihar Neja yaga hanyar da aka zuba makurden kudi aka gyara yanzu kuma aka lalata dole ne yayi magana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: