Jiya ba Yau ba: Hotuna 6 na shugaba Buhari
Kowa ya san cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari tsohon soja ne, kuma shi soja ai baya canjawa, ko ba jima, ko ba dade.
Da haka ne wannan rahoton yayi kokarin gano bambamcin shugaba Buhari a yau, da zamanin da yayi mulkin soja, ko daga kallon fuska ma zaka iya gano akwai bambamci da dama, duba da lokacin da yake soja, da yanzu.
Ga wasu hotuna da zasu rantsar da kai:
1. Buhari dan matashi
Kunga tsalelen saurayi, son kowa kin wanda ya rasa!
2. Shugaba Buhari
Dawainiyar mulki ya fara nunawa a jikin shugaban kasa Buhari
3. Har cikin kayan Nasara
An dauki hotunan nan shekaru aru aru tsakanin su, amma bambamcin su kadan ne kawai, Buhari kenan!
KU KARANTA:Labari da dumi: Boko Haram ta sako yan matan Chibok 21
4. Buhari cike da buri
Kyakkyawan siffar shugaba Buhari mai karko ne, su Buhari an dade ana fantamawa
5. Soja ne ko Farar hula?
Wane ka zaba?
6. Soja marmari daga nesa
Buhari a soja sanye da kayan sarki, sa’annan ga shi sanye da kayan kabilar inyamurai. Amma fa sojan na nan.
Asali: Legit.ng