Wani mutumi ya kashe kansa saboda talauci

Wani mutumi ya kashe kansa saboda talauci

- Wani mutumi mai shekaru 60 a Ughelli jihar Delta Okporo Arigo, ya rataye kansa a kan wani bishiya, bayan ya bar wani takarda dauke da dalilin da yasa ya aikata hakan

- An gano Arigo wanda kaninsa ke aiki a matsayin kansila a arewacin Ughelli a daji tare de takarda kusa da gawarsa dake rataye

Wani mutumi mai shekaru 60 a Arewacin karamar hukumar Ughellii dake jihar Delta ya kashe kansa, ya bayyana rashin iya ciyar da iyalinsa da biya masu bukatunsu a matsayin dalilin da yasa ya aikata hakan a kansa.

An bayyana cewa wanda abun ya faru dashi, Okporo Arigo, ya rataye kansa a jikin wani bishiya ya kuma bar takarda wanda ya bayyana dalilin da yasa ya yanke ma kansa wannan mummunan  hukuncin, jaridar Nation ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Likita ya cire tsutsotsi 80 daga kunnen wata yarinya

Anga Arigo wanda kaninsa ke aiki a matsayin kansila a arewacin Ughelli, a daji tare da takarda dake bayyana dalilin mutuwarsa a kusa da gawarsa dake lilo a sama.

Wani mamba na karamar hukuman Uwheru, wanda yayi Magana kan halin da ya haddasa al’amarin yace takardan da wanda ya aikata kisan ya bari yayi ikirarin cewa abunda ya haddasa shi aikata kisan shine sakamakon kasa ciyar da iyalisa da kuma kasa daukar nauyin bukatunsu.

Wata majiya ta bayyana cewa gwamnatin jihar bata biya kanin Arigo kudin albashi ba tun tsawon watanni 10 da suka wuce.

Tunda kasar Najeriya ta shiga halin koma bayan tattalin arziki, an samu yawan kisan kai da dama sakamakon matsin rayuwa a kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng