Matashi ya tuttuka kashi a kotu

Matashi ya tuttuka kashi a kotu

Wani abin ban mamaki da ban dariya ya faru jiya Talata 11 ga watan Oktoba a kotun majistri na Benin lokacin da wani mai laifi dan shekara 18 mai suna Abdullahi Muhammed yayi tuttuka kashi yayin da aka kira sunansa ya fito don amsa tambayoyi.

Matashi ya tuttuka kashi a kotu

Sai dai bayan Abdullahi ya kammala kashin, sai ya gyara wandonsa ya fita a sittin, ya ruga waje da niyyar guduwa, wanda hakan ya kawo rudani a bainar kotun.

Da ganin haka ne, sai dansanda mai kara Sajan Aigbochie Iruonagbe ya saka ihu yana neman taimako daga jama’a dasu taimake shi wajen kama Abdullahi mai kasha. Nan da nan kuwa jama’a suka yi ma Abdullahi tara tara aka kama shi, bayan an kama shi ne yansanda suka bashi ruwa yayi tsarki, daga bisani aka cigaba da sauraron karar sa.

KU KARANTA: Naira tayi daraja a kasuwannin bayan fagge

Da fari dai an gurfanar da Abdullahi ne kan laifin satar kwalaye hudu na madarar gari daga shagon wata mata mai suna Favour Nwachukwu a ranar 8 ga watan Oktoba. Sai dai Abdullahi ya amsa laifinsa, daga nan sai alkali ma shari’a JO Ejale ta daga sauraron karar  zuwa 14 ga watan Oktoba.

Idan ba’a manta ba, a baya ma an samu wani mutum Joe Chinakwe daya rada ma karansa suna Buhari, inda aka kama shi, aka gurfanar da shi gaban kotu kan laifin kawo rikici tsakanin al’umma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng