Gwamna Umahi ya sayi motocin naira miliyan 19
Gwmnan jihar Ebonyi David Umahi ya siya ma ilahirin kwamishinoninsa motoci da duk daya ta kai naira miliyan 19, inji rahoton jaridar Gaurdian.
A jiya litinin 10 ga watan Oktoba ne Gwmna Umahi ya mika ma kwamishinonin sa makullan motocin a garin Abakalake, inda yace yayi hakan ne don ya kara musu kwazo.
Umahi yace, sun fara cinikin siyan motocin ne tun dala na daidai da N300, amma biyo bayan tashin dala ne sai farashin ya koma N19m. idan za’a tuna, a kwanakin baya ma gwamna Umahi ya baiwa dukkanin yan majalisun jihar su 24 irin wannan motar.
KU KARANTA: Super Eagles sun sha da kyar daga harbin bindiga
Kazalika su ma masu baiwa gwamna shawara sun samu nasu rabon motocin a watannin kadan da suka gabata. Kimanin wata daya kenan ministan kimiyya da fasaha Dakta Ogbonnaya Onu ya mayar ma Gwamna Umahi kyautan motar daya bashi. Ministan ya bayyana dalilinsa na mayar da kyautan da cewa tsarin mulki bai sanya shi cikin wadanda aka yarda jiha ta siyan ma mota ba.
A wani labarin kuma, hukumar yaki da zamba da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta kama kanin gwmana Umahi, Austin Umahi dangane da rawar daya taka yayin rabon kudaden cin hanci da aka raba a zabukan 2015.
Asali: Legit.ng