Gwamnan jihar Delta ya yanke jiki ya fadi

Gwamnan jihar Delta ya yanke jiki ya fadi

- An rahoto cewa gwamnan jihar Delta ya kife a ofishinsa a makon da ya wuce

- Yayin da wasu majiya suka tabbatar da ci gaban, kakakin Okowa ya karyata al’amarin

Gwamnan jihar Delta ya yanke jiki ya fadi

Sahara Reporters ta samu bayanin cewa Gwamnan jihar Delta Ifeanyi Okowa, ya yanke jiki ya fadi a gidan gwamnati a ranar Laraba 5 ga watan Oktoba.

Wani majiya daga gidan gwamnati, wanda ya bukaci a boye sunansa, ya bayyana cewa gwamnan ya shirya zuwa taron murnar ranar malamai ta duniya a ranar Laraba da ta wuce.

A halin da ake ciki, bayan an gama duk shirin da ya dace, an rahoto cewa Okowa ya yanke jiki ya fadi a ofishin sa wanda hakan ya hana sa halartan taron.

Majiyar ya ci gaba da bayyana cewa a take aka dauke gwamnan daga ofishin nasa zuwa wani guri da basu sani ba don samun kulawar likta sannan kuma aka bukaci mataimakinsa Kingsley Otuaro da ya wakilce shi a gurin taron.

KU KARANTA KUMA: Dalilin da zai iya sa yan Najeriya kin APC a 2019

Patrick Ukah, kwamishinan bayanai na jihar, baya daukar kiran sa, yayinda babban sakataren labaran gwamnan, Charles Aniagwu ya karyata labarin da ake ikiri cewa ba gaskiya bane.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda yayi tafiyar kwanaki 10 birnin Landan don ganin likita a watan Yuni, zai kuma ziyarar kasar Jamus a ranar 12 ga watan Oktoba don kuma duba lafiyar sa.

A halin yanzu, ba’a san wani irin rashin lafiya Buhari zai je magani ba ko kuma dai kawai zuwa ganin likita zaiyi don ya duba sa.

Shugaban kasar bai rigada ya sanar da sabon ziyarar ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel