Anga Korede Bello tare da Gumsu Sani Abacha

Anga Korede Bello tare da Gumsu Sani Abacha

- An fitaccen jarumin Mavin Record ya fita tare da Gumsu Sani Abacha

- Tana daya daga cikin yaya matan marigayi tsohon shugaban kasa a mulkin soja, Sani Abacha

Anga Korede Bello tare da Gumsu Sani Abacha

Korede Bello ya kasance babban mawakin Najeriya wanda ke aiki da Mavin Record a yanzu. An fi saninsa a cikin wani waka da yayi mai taken Godwin wanda ya samu karbuwa sosai a masana’antar wakar Najeriya.

KU KARANTA KUMA: Masoya sunyi baiko bayan soyayyar shekaru 10

A jiya Litinin 10 ga watan Oktoba, an ga mawakin dake tashe tare da daya daga cikin yaya matan marigayi tsohon shugaban kasar Najeriya a mulkin soja, Sani Abacha. Yarinyar ba wata bace illa Gumsu Sani Abacha sun kuma yi hotuna da dama tare da jarumin cikin annashuwa da walwala.

Kalli hotunan a kasa:

Anga Korede Bello tare da Gumsu Sani Abacha
Korede Bello tare da Gumsu Sani Abacha

KU KARANTA KUMA: Dailin da yasa Arewa suka juya ma Jonathan baya

Ya rubuta a jikin hoton #mummybellover don nuna ta a matsayin masoyiyarsa a fannin waka. Gumsu tayi aure da yara biyar kuma da alama sun ji dadin lokacin da suka kasance tare.

Korede na tashe sosai kuma a hankali ya fara daukaka zuwa shekaru mai fadi ba wai a tsakanin matasan yan mata kawai ba. Muna fatan ya ci ma manufarsa na son kasancewa a babban matsayi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel