Ronaldo ya kafa muhimmin tarihin duniya
Cristiano Ronaldo ya zura kwallaye hudu a wasan da Portugal ta doke Andorra 6-0 domin neman cancantar shiga gasar cin kofin duniya ta 2018.
Su ma kasashen Belgium da Faransa sun yi nasara a wasannin da suka yi. Ronaldo ya zura kwalle biyu minti hudu da fara wasan. Joao Cancelo ya kara kwallo ta uku, yayin da Ronaldo kara kwallaye biyu.
Dan wasan Andorra Andre Silva ya ci gidansu duk da cewa an fitar da 'yan wasan kungiyar biyu daga wasa saboda sun yi laifi.
Yanzu dai Portugal ce ta uku a rukunin B saboda shan kashin da ta yi a hannun Switzerland, wacce kuma ta doke Hungary da ci 3-2 a wasan da suka yi ranar Juma'a.
Ronaldo ya ji rauni a wasan karshe na gasar Euro 2016 - kuma wannan ne karon farko da yake yi wa kasarsa wasa tun bayan gasar, wacce Portugal ta lashe da ci 1-0.
Dan wasan ya ce: "Na san ina da matukar muhimmanci, kamar yadda sauran 'yan wasa suke. Na yi bakin mkokarina ga kasata. Ina jin dadin komowa murza leda tun bayan raunin da na ji a gasar cin kofin turai. Za mu buga wasanni takwas, kuma ina son mu lashe dukkansu ta yadda za mu samu zuwa gasar cin kofin duniya."
Asali: Legit.ng