Yadda aka kama mutumin da ya saci Yarinya Sultaana
- Mun kawo labarin yadda wani mutumi ya sace wata karamar yarinya mai suna Sultaana a garin Kaduna
- An kama wannan mutumi ya sace Sultaana da Nasir
- Yanzu haka wadannan mutune suna hannun ‘yan sanda a jihar Kaduna
Mun kawo rahoton yadda aka kama wani mutumi ya sace wata yarinya Sultaana. A wannan karo mun kawo maku cikakken labarin yadda wannan abu ya auku bayan mun yi magana da iyayen wannan yarinya ta wayar Tarho. An sace wannan yarinya Sultana watau Zainab Umar watanni bakwai da suka wuce. Da yake abin da rabo sai ga shi an gan ta a karshen wannan mako. An sace Sultaana ne a Badiko yayin da za ta je Makarantar Islamiyya. Bayan dai har iyaye sun saduda, an fawwalawa Ubangiji, kwatsam sai ga Sultaana ta dawo.
Bayan an sace ta daga Badiko, an yi kokarin canza mata unguwa zuwa Malali, a can kuwa wata rana ‘Yar uwar iyayen yarinya suka hadu da matar da ta ke dauke da su. Abin ya faru ne lokacin wannan mata tana cikin Keke Napep, kawai sai ta hango Sultaana, nan take, tace da mai babur ya hanzarta wajen wancan mata. Sai ga mata Inyamura da yaran hausawa har biyu suna tafiya, nan kuwa mata tace ai wannan diyar mu ce da aka sace. Inyamura tace Allan-barin ‘Ya ‘yan ta ne- ‘Na my pikin’ domin ba ta ko jin Hausa. Nan fa mata ta tara Jama’a, har ta kai tace idan ana so a gane, a duba hannun yarinya inda ta taba konewa, ana dubawa, sai ga shaida kuwa, daga nan sai wajen ‘Yan sanda kaya-kaya.
KU KARANTA: An gano Sultaana bayan watanni bakwai da sace ta
Ko da aka je ga Hukuma sai mijin wannan mata wanda asalin sa mutumin Yola ne, ya bayyana cewa hakikanin gaskiya, ba diyar su bace. Ya ji tsoron idan ya fada a waje, za a masa illa. Wannan mutumi ya bayyana cewa shi dai yana da sha’awar yara mata, tun da bai haifa ba, sai ya ga Sultaana wata rana ya dauke ta. Har kuwa ya sa ta a makaranta, ana kuma mata darasi a gida, ya saya mata kayan wasa, har da wani keke na kusan dala dubu, ga lalle ta sha rangadau. Shi kuma Nasir-wanda har an sauya masa suna zuwa Ibrahim, wani yaro ne da ya sato shi ma, mahaifin sa kuma yaron Tsohon mataimakin Shugaban Kasa Namadi Sambo ne.
A gidan wannan mutumi dai an samu wasu yaran manya masu kimanin shekaru 16; akwai mai koyawa yara-Su Sultaana karatu, akwai mai gadi da kuma wani mai aikace-aikace. Tuni dai har wannan mutumi yayi wa yaran nan Fasfo na Kasar waje, yace kuma sana’ar sa kasuwanci daga Dubai zuwa Najeriya. Matar sa kuma Inyamura, yace ta musulunta ne. Tuni dai har Gwamnan Jihar Malam Nasiru El Rufai ya leka wurin.
Asali: Legit.ng