Femi Falana yayi kaca-kaca da rubabbun Alkalai

Femi Falana yayi kaca-kaca da rubabbun Alkalai

Wani Babban Lauya a kasar nan watau Femi Falana yace kama manyan rubabbun Alkalan kasar da akayi yayi kyau

Femi Falana ya kira Gwamnati da tayi maza ta hukunta su, sannan kuma ya caccaki Kungiyar NBA ta Lauyoyin Kasa

– Mista Femi Falana yace ai maganin Alkalan kenan

Femi Falana yayi kaca-kaca da rubabbun Alkalai

Wani Babban Lauya a Kasar nan wanda yayi fice Mista Femi Falana SAN yace kama manyan Alkalan Kasar da akayi cikin wannan makon yayi daidai. Babban Lauya Femi Falana ya kuma soki Kungiyar Lauyoyi na Kasar ta NBA da kokarin kare rubabbun Alkalai.

A karshen wannan makon ne dai Jami’an farar kaya na DSS suka burma gidan wasu daga cikin manyan Alkalan Kasar nan. Mutane da dama sun soki wannan aiki da Hukumar DSS tayi, abin da ma Jam’iyyar adawa ta PDP ta ce ashe gara Marigayi Janar Abacha da Shugaba Muhammadu Buhari. Kungiyar Lauyoyi na Kasa watau NBA ba ta ji dadin wannan abu ba, ta nemi a saki Alkalan ba da wata-wata ba.

KU KARANTA: Kaji makudan kudin da DSS ta karbe gidajen Alkalai?

Sai dai Jaridar Punch ta rahoto shi wannan babban Lauya da aka sani Femi Falana yayi kaca-kaca da Kungiyar NBA ta Lauyoyi, yace tana kokarin kare bata-garin Alkalai. Femi Falana yace sau da yawa an saba zargin Alkalan Kasar da rashin gaskiya, sai dai ba abin da ake iya yi, asali ma iyakar ta ayi masu ritaya.

Babban Lauya Femi Falana ya ce dole Gwamnati da tayi maza ta kai Alkalan Kotu, sannan kuma suna da damar beli kamar kowa.

 

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel