Jami’an DSS sun far ma Alkalan Kotun koli
– An damke Alkalan kotun kolin Najeriya guda 2 da laifin alkalancin zalunci
– Daya daga cikin iyalan Alkalan ya ci bugu yayinda suka kai harin inda suka fasa gidajen da guduma
Rahotanni da aka samu daga Abuja na nuna cewa jami’an Department of State Security (DSS) sun far ma Alkalan Kotun koli guda 2 a Abuja.
Game da rahoton Sahara Reporters, Alkalan da abin ya shafa sune Nnamdi Dimgba da Adebiyi Ademola,wadanda akayi ma gidajen su zobe a daren ranan Juma’a.
KU KARANTA: An kama mawakin coci da yunkurin sace mota SUV
Gida ta 32 da 34 a Samuel Ogbemudia Crescent a Apo Legislative Quarters inda yan uwan Alakalan ke zaune ma bata tsira ba yayinda jami’an sukayi ma wani dan uwan Dimgba dukan tsiya.
Wata majiya ta bayyana cewa dalilin da yasa DSS tayi hakan shine nuna rashin jin dadin ta da wasu shari’a da wadannan Alkalan sukayi da kuma sukan DSS ta Dimgba yayi.
An bada rahoton cewa Nyesome Wike ya hana wasu jami’an DSS da yan sanda damke wani alkali a gidansa dake 35 /84 B residence, Forces Avenue, Port Harcourt.
Jaridar Legit.ng ta bayyana cewa Diraktan DSS na jihar Ribas Mr Tosin Ajayi, da kwamishanan yan sandan jihar Ribas, Mr Francis Odesanya ne suka hana a kama Alkalin
A cewar wanda abun ya faru a kan idanunsa, jami’an tsaro sun tare hanyan shiga gidan Alkalin misalign karfe 1 na dare kuma sun ce sun yi hakane bisa ga umurni.
Asali: Legit.ng