Iyayena Mutanen Sokoto da Jigawa ne don haka ni ‘Dan Najeriya ne – Inji Atiku
‘Dan takarar shugaban kasa a zaben 2019, Atiku Abubakar, ya maidawa martani a game da ce-ce-ku-cen da ake yi na cewa asalin sa mutumin kasar Kamaru ne don haka bai halatta ya fito takara ba.
Jaridar Daily Nigerian ta rahoto Alhaji Atiku Abubakar ya fadawa kotun da ke sauraron karar zaben 2019 cewa Iyayensa ‘Yan Najeriya ne don haka shi ma ya zama cikakken ‘Dan Najeriya, a sakamakon asalin Mahaifan na sa.
Atiku Abubakar ya sanar da kotu cewa wanda ya haife sa Garba Atiku Abdulkadir ya fito ne daga kasar Wurno wanda ta ke cikin jihar Sokoto a yau. An haifi Atiku ne a 1946 a cikin Garin Jada da ke tsohuwar Kasar Kamaru.
‘Dan takarar na PDP ya kuma ce Mahaifiyarsa Aisha Kande, asalin ta Mutumiyar Garin Dutse ce, wanda yanzu nan ne babban Birnin Jihar Jigawa. APC tana ikirarin cewa Atiku ba ‘Dan kasa bane don haka bai da hurumin takara.
KU KARANTA: Sanatan Najeriya ya gargadi Malamai da shiga cikin aikin zabe
Lauyoyin Atiku sun fadawa Kotu cewa da shi da Muhammadu Buhari duk Fulani ne, kuma Iyayen Atiku sun bar Sokoto ne a dalilin yawan fataucin da ya kai Kakanninsa zuwa Garin Jada a dalilin wani Abokinsa mai suna Ardo Usman.
Masu kare Atiku a gaban kuliya sun fadawa kotu cewa Kakan ‘dan takarar na PDP na wajen Ubansa ya haifi Mahaifinsa Garba a Garin Jada ne bayan sun yi kaura daga kasar Sokoto saboda harka ta kasuwanci a zamanin da.
Haka zalika Lauyoyin ‘dan takarar sun bayyana cewa Kakannin Mahaifiyarsa watau Aisha Kande sanannun ‘yan kasuwa ne a cikin Jigawa a wancan lokaci. Lauyoyin su kace Kakan Atiku ta wajen Uwa sunan sa Malam Inuwa Dutse.
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng