Sabon Farashin Man Fetur
Ministan Ma’adanai, Dele Alake, ya ce Bola Tinubu ya nuna karfin guiwa inda ya dauki manta da siyasa wajen cire tallafin man fetur da ya jawo matsala.
Yan takarar gwamnan jam'iyyar ADC) a jihohi bakwai na yankin Arewa maso Yamma sun bukaci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya janye matakin cire tallafin fetur.
Kenneth Okonkwo, kakakin kwamitin kamfen Atiku Abubakar, ya ce duk wanda ke goyon bayan ci gaba da sayar da fetur kan N1,300 bai cancanci jagorantar Najeriya ba.
Rahotanni sun nuna cewa farashin fetur na ci gaba da tashi gidajen mai a Najeriya duk da raguwar farashin da ake sayar da shi a wuraren ajiya watau farashin sari.
Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya sun bukaci dawo da tallafin man fetur, biyan basussukan albashi da alawus, da tallafin tsadar rayuwa domin rage matsin tattalin arziki.
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APM, Gwamna Seyi Makinde, ya yi watsi da batun dawo da tallafin man fetur, ya ce an ma kalamansa gurguwar fahimta.
Atiku Abubakar ya zarge Bola Tinubu da jefa 'yan Nijeriya a matsi ta hanyar tsarin tallafin mai da ke gurgunta kasuwanci tare da samar da alheri ga abokansa kawai.
Dan takarar shugaban ƙasa na SDP, Adewole Adebayo, ya yi alkawarin rage farashin man fetur, gas da Jet A1 zuwa N200 kan lita idan ya lashe zaɓen 2027.
Farfesa a Jami'ar Obafemi Awolowo (OAU), Tunji Ogunyemi, ya ce jihohi 15 na Arewacin Najeriya za su durkushe cikin watanni uku idan aka dawo da tallafin man fetur.
Sabon Farashin Man Fetur
Samu kari