Zaben Shugaban kasan Najeriya
Tsohon mai magana da yawun kwamitin yaƙin neman zaben shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Daniel Bwala ya koma jam'iyyar APC mai mulki, ya gana da Tinubu.
Yan Najeriya na tsaka da bayyana rashin gamsuwa da yadda Bola Tinubu ke mulkar kasar, sai ga shi an fara shirye-shiryen ya sake tsayawa takara a 2027.
Kungiyar matasa masu goyon bayan Atiku, NYFA, ta ce tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar zai kawo sauyi ga al’ummar kasar idan ya zama shugaban kasa.
An yi ikirarin cewa shugabar kotun daukaka kara mai shari'a Monica Dongban-Mensem tace an ba alkalan kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa na 2023 cin hanci.
Mataimakin shugaban jam'iyyar Labour Party (LP), Ayo Olorunfenmi, ya bayyana cewa a jam'iyyar ne kadai Peter Obi zai samu nasarar lashe zaben shugaban kasa na 2027.
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya kai ziyara ga fitattun shugabannin kasar nan da suka hada da Buhari, Janar Babangida, da Abdulsalami Abubakar.
Kasim Balarabe Musa ya jagoranci wata zanga-zangar lumuna a Kaduna inda aka ji ya ce abubuwa ba su taba kai haka ba, idan Bola Tinubu ba zai iya ba ya sauka.
Hadimin shugaba Bola Ahmed Tinubu na musamman kan kafafen sada zumunta, Dada Olusegun ya magantu kan bidiyon faduwar shugaban kasa a yayin bikin ranar dimukuradiyya.
Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu zai gana da 'yan Najeriya ta cikin jawabi a ranar dimukuradiyya. A gobe ne za a yi bikin ranar.
Zaben Shugaban kasan Najeriya
Samu kari