Zaben Edo
Dan takarar jam'iyyar PDP a zaben Edo, Asue Ighodalo ya yi korafi kan neman karya shi da ake wurin rashin kawo kayan zabe a kan lokaci a mazabun da ya fi karfi.
A yau ne za a gudanar da zaben gwamnan jihar Edo da ke Kudu Maso Kudancin Najeriya, zaben dai zai ja hankali musamman a tsakanin ƴan takarar PDP, APC da LP.
Yayin da zabe ya kankama a mafi yawan rumfunan zaɓe, Asur Ighodalo ya bayyana damuwa kan abin da ya kira barazanar tsaro a sassan jihar yau Asabar.
Jam'iyyar PDP ta yi kira da babban Sufeto Janar na 'yan sandan Najeriya, Kayode Egbetokun da ya janye AIG shiyya ta bakwai daga aikin zaben gwamnan Edo.
Olumide Akpata ya bayyana cewa kawo yanzu ya samu bayanai marasa daɗi dangane da zaben gwamnan da ke gudana a jihar Edo, ya ce zai bincika lamarin.
Sabuwar rigima ta barke a wata rumfar zabe da ke karamar hukumar Orhionmwon ta jihar Edo a ranar Asabar bayan da jami'an INEC suka manta da takardar rubuta sakamako.
Rahotanni sun bayyana cewa jami'an hukumar EFCC sun cika hannu da wasu mutane uku da ake zargin suna sayen kuri'u a yayin da ake gudanar da zaben jihar Edo.
Kwamishinar hukumar zabe a jihar Edo, Farfesa Rhoda Gumus ta ce ko nawa aka kawo mata na cin hanci ba za ta taɓa karba ba domin kare mutuncinta da take da shi.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta bayyana cewa za ta dora sakamakon zaben gwamnan jihar Edo a kan na'urar IReV idan babu matsalar sabis.
Zaben Edo
Samu kari