Matsin tattalin arziki
Bankin duniya ya ce an samu koma bayan haɓakar tattalin arzikin Najeriya a lokacin mulkin Muhammadu Buhari. Bankin duniya ya ce an samu barna a lokacin Buhari.
Shugaban majalisar dattawa, Godswill Apkabio ya tabbatarwa yan kasar nan cewa ba a gwamnatin Bola Tinubu aka fara samun matsalar tattalin arziki ba
Gwamnatin tarayya ta sanya harajin kashi biyar kan ayyukan sadarwa, wasanni, da wasu nau'ikan caca a matsayin wani kudiri na kawo sauyi ga tsarin harajin Najeriya.
Gwamna Nasir Idris Kauran Gwandu ya kafa kwamiti na musamman da zai gudanar da bincike domin dawowa da marayu hakkinsu da aka danne a jihar Kebbi.
Kusa a APC ya yi kuka kan yadda lamura ke tafiya a mulkin Bola Tinubu. Jigon APC ya koka kan yadda darajar Naira ta karye da yadda ake nuna son kai a Najeriya
Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual, Primate Babatunde Elijah Ayodele ya ce gwamnatin Najeriya ta san ba za ta iya magance matsalar tattalin arziki ba.
Musa Iliyasu Kwankwaso ya ce lokacin tsayawa nuna adawa da sukar juna ya wuce, ya kamata su Atiku da Obi su shigo a tafi tare don ceto ƴan Najeriya daa ƙunci.
Sanata mai wakiltar Abia ta Arewa, Orji Kalu ya ce shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya na sane da halin da kasar nan ke ciki domin ya na shiga mutane.
Ministan kasafin kudi da tsare-tsare.na kasa, Abubakar Atiku Bagudu ya bayyana cewa dole yan kasar nan su sake lissafi wajen yin cefane domin babu kudi a kasa.
Matsin tattalin arziki
Samu kari