Matsin tattalin arziki
Yayin da ake kuka bayan karin kudin mai a fadin Najeriya, gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun ya kawo hanyar saukakawa al'ummarsa bayan karin kudin mai a kasar.
Gwamnatin jihar Zamfara ta amince da gina sabuwar kasuwar zamani a Gusau kan Naira biliyan 3.6. An ce za a kammala aikin a cikin watanni 12 bayan ba da kwangilar.
Babbar kotun tarayya mai zama a Abuja ta amince da buƙatar belin masu zanga zanga 10 da ake tuhuma da cin amanar ƙasa, ta gindaya masu sharuɗdan beli
Shugaban Yarabawa, Iba Gani Adams ya tura wasika ga Bola Tinubu yana caccakansa kan yadda ya mayar da Najeriya cikin kasa da shekaru biyu ana wahalar rayuwa.
Rahotanni sun bayyana cewa fasinjoji a Kaduna sun koma hawa jirgin kasa duk da fargabar rashin tsaro sakamakon tsadar motocin haya biyo bayan karin kudin fetur.
Primate Elijah Babatunde Ayodele ya fitar da wani sabon hasashe a game da wahalhalun da ‘yan Najeriya ke ciki a karkashin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.
Kungiyoyin Arewa da Kudu sun bukaci Bola Tinubu ya rage kudin man fetur. Hausawa, Yarabawa da Ibo sun yi magana ga gwamnatin tarayya da murya daya.
Kungiyar kwadago ta bukaci Bola Tinubu ya rage kudin mai, rage kudin wutar lantarki, sake shugaban kwadago, Joe Ajearo da kuma fara biyan sabon albashi na N70,000.
Tsohon mai magana da yawun Goodluck Jonathan, Dakta Reuben Abati ya ce yanzu haka tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari na can yana yiwa Najeriya dariya.
Matsin tattalin arziki
Samu kari