
Hukumar DSS







Rahotanni sun bayyana cewa jami'an tsaron farin kaya na DSS sun ci karo da miyagun makamai da alburusai a ofishin tsohon shugaban majalisar jihar Legas.

Jami’an hukumar DSS da na rundunar 'yan sanda sun mamaye zauren majalisar dokokin jihar Legas, inda suka rufe ofisoshin kakakin majalisar da wasu shugabanni.

Shugaban kamfanin hada hadar kudin crypto watau Binance ya lissafa sunayen ƴan Majalisar wakilan tarayyar Najeriya 3 da suka nemi cin hancin dala miliyan 150.

SERAP ta bukaci Shugaba Tinubu ya binciki batan Naira biliyan 26 daga PTDF da Ma'aikatar Man Fetur a 2021, tare da mayar da kudaden don rage gibin kasafin kudi.

Hukumar tsaro ta farin kaya ya shiga rikicin masallacin Jami'ur Rahaman, wanda aka fi sani da Masjid Sahaba, inda aka gayyaci babban malamin nan, Bin Uthman.

Jami'an DSS sun kama wani matashi da ya shigo da makamai daga Nijar zuwa Nijar. Matashin ya tsere yayin da sojoji suka nemi kama shi kafin a kamo shi daga baya.

Jami'an tsaro na hukumar DSS sun samu nasarar cafke wani hatsabibin mai safarar makamai a jihar Zamfara. Jami'an na DSS sun cafke shi ne bayan samun bayanan sirri.

Hukumar ƴan sandan farin kaya watau DSS ta gurfanar da sanannen ɗan gwagwarnayar nan Mahdi Shehu a gaban kotu, ta tuhume shi da laifukan ta'addanci.

Matar Benjamin Ezemma ta roƙi jami'an tsaro su gano mijinta da aka sace a Anambra, tana nuna damuwa game da yadda ake gudanar da bincike kan batansa.
Hukumar DSS
Samu kari