Babban bankin Najeriya CBN
A labarin nan, za a ji dalilin da gwamnatin tarayya ta bayar na shirn karbo rancen $24bn daga bankuna da hukumomi daban daban na duniya, ta ce kowa zai amfana.
Babbar kotun tarayya mai zama a Kano ta yanke wa Murja Kunya hukuncin ɗaurin watanni 6 a gidan yari ko tarar N50,000, ta bukaci a naɗa ta jakadar CBN da EFCC.
Gwamnatin tarayya za ta sayar da gidaje 753 da aka kwato daga Godwin Emefiele, ta hanyar yin gwanjonsu a shafin Renewed Hope na intanet, bayan umarnin kotu.
Wata babbar kotu ta yanke wa 'yan TikTok biyu hukuncin daurin watanni shida a Legas saboda wulakanta Naira. EFCC ce ta gurfanar da su bayan samun bidiyo.
Bankin duniya ya saki kudi har Dala miliyan 125 a cikin rukunin lamunin da zai rika ba kasar domin rabawa talakawa. Za a raba rancen ne domin rage radadi.
Majalisar wakilai ta gayyaci ministocin Bola Tinubu 2, gwamnan CBN, da Akanta Janar ranar Talata mai zuwa kan gaza biyan kudin 'yan kwangila tun shekarar 2024.
Najeriya ta kammala biyan bashin dala biliyan $3.4 daga IMF, wanda aka karba a 2020 don tallafin Korona; yanzu ba ta cikin jerin kasashen da ake bi bashi.
Bankin Duniya ya bukaci Najeriya ta kare talakawa daga hauhawar farashi, ta samar da ayyukan yi, da amfani da kudin man fetur don rage talauci a cikin jama'a.
Bankunan Najeriya sun kara cajin kudin tura sakon kudi daga N4 zuwa N6 daga yau Alhamis 1 ga Mayu. Sun yi karin ne saboda karin kudin sadarwa da aka yi a Najeriya.
Babban bankin Najeriya CBN
Samu kari