Atiku Abubakar
Shugaban ma'aikatar fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila ya yi kira ga Leke Abejide da Nafiu Bala da su tsaya su tarwatsa jam'iyyar adawa ta ADC.
Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya fito ya yi martani kan sukar da Alhaji Atiku Abubakar ya yi wa gwamnatinsa. Ya ce kowa yana yin kuskure.
Mai magana da yawun ADC na kasa, Bolaji Abdullahi ya ce bayan Kwankwaso, akwai kusoshin siyasa da za su hade da Atiku, Peter Obi da sauran yan hadaka.
Jam'iyyar ADC mai adawa ta yi magana kan batun cewa tana shirin hadewa da PRP. Ta bayyana cewa ko kadan babu kamshin gaskiya a batun kawancen da ake yadawa.
Tsohon ɗan majalisar tarayya a Najeriya, Abubakar Yusuf ya bayyana cewa APC ba ta jin ko ɗar a kan ko za ta faɗi babban zaɓen 2027 duk da haɗa kan ƴan adawa.
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa jam'iyyar ADC ta zama jam'iyyar da ta shirya kawar da APC daga madafun iko a zaben 2027.
A labarin nan, za a ji aikin da Shugaba mai ci, Bola Ahmed Tinubu da sauran wadanda ke da niyyar neman kujerar shugaban kasa a 2027 suka fara yi wa ƴan ƙasa.
Tsohon gwamnan Sakkwato kuma jagoran ADC a jihar, Sanata Aminu Waziri Tambuwar ya ce jam'iyyar za ta share hawayen yan Najeriya idan ta kafa gwamnati.
Shugaban tsagin jam'iyyar ADC na kasa, Nafiu Bala, ya yi zarge-zarge kan tsohon dan takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Atiku Abubakar
Samu kari