APC
Jam'iyyar APC ta ci karo da cikas da daruruwan magoya bayanta da na LP suka watsar da jam'iyyunsu inda suka da koma PDP a jihar Edo ana shirin zabe.
Shugaban kasa, Bola Tinubu ya tura sakon ta'aziyya ga iyalan marigayi Sanata Ifeanyi Ubah da abokansa da ma al'umma da gwamnatin jihar Anambra kan wannan rashi.
Jam'iyyar APC ta goyi bayan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu yayin da masu niyyar zanga-zanga ke shirin farawa a fadin kasar nan. Ta ce akwai kuskure a bukatunsu.
An shiga jimami a Najeriya bayan sanar da mutuwar Sanata Ifeanyi Ubah da ke wakiltar Anambra ta Kudu a Majalisar Dattawa a birnin Landan da ke Burtaniya.
Shugaban jam'iyyar APC, Abdullahi Ganduje ya kira wata ganawa da shugabannin APC a jihohi 36 a kasar yayin da ake shirin shiga zanga-zanga na halin kunci.
Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta ba na hannun daman Ministan Abuja, Nyesom Wike mukami a kwamitin kamfe na zaben jihar Edo da za a yi a watan Satumbar 2024.
Sanata Muhammad Ali Ndume ya bayyana cewa ba zau bar APC matukar Gwamna Babagana Zulum na cikinta, ya bayyana cewa da shi aka kafa jam'iyyar tun asali.
Sakataren jam'iyyar APC ya bayyana cewa gwamnatin Bola Tinubu na bakin kokarinta wajen shawo kan matsalolin tattalin arziki yayin da ya musanta rahoton NBS.
Kungiyar gwamnonin APC ta ce babu dalilin yin zanga-zanga a dai-dai wannan lokaci inda ta ce ba ta san musabbabin hakan ba tare da kiran a zauna a teburin sulhu.
APC
Samu kari