Abun Bakin Ciki
Rahotanni sun ce kusan kullum sai an samu mace mace a asibitin IDH na Kano sakamakon barkewar sabuwar cutar mashako. zuwa yanzu mutane akalla 40 sun mutu.
An sanar da rasuwar kwamishinan yan sanda a jihar Akwa Ibom, Waheed Ayilara da safiyar yau Alhamis 29 ga watan Agustan 2024 a Lagos bayan fama da jinya.
Kwanaki hudu kacal da rasuwar Sarkin Ningi, Alhaji Yunusa Danyaya, masu nadin sarauta a masarautar sun rubuta wasiku ga masu sha'awar neman kujerar marigayin.
A jiya Talata 27 ga watan Agustan 2024 aka sanar da rasuwar fitaccen jarumin fina-finan Nollywood, Yusuf Olorungbede bayan ya sha fama da jinya na tsawon lokaci.
Gwamnatin jihar Sokoto ta ce biyan kudin fansa domin karbo sarkin Gobir daga hannun 'yan bindiga ya sabawa dokar yaki da ta'addanci ta Najeriya da aka kirkira a 2023
Kwamishinan kudi na jihar Borno, Ahmed Ali Ahmed ya kwanta dama. An ce ya rasu ne a safiyar yau Litinin, 26 ga Agustan 2024 a cikin gidansa da ke Maiduguri.
Mutum ɗaya ya rasa ransa a karshen makonnan a jihar Bayelsa lokacin da wani jirgin ruwa ya kife bayan ya ɗauko mutane a yankin karamar hukumar Ijaw ta Kudu.
Sanata Aminu Waziri Tambuwal ya kaɗu bayan rashin da ya tafka na kaninsa, Alhaji Ahmad Ibrahim Tambuwal a jiya Asabar 24 ga watan Agustan 2024 a birnin Abuja.
A wannan labarin za ku ji cewa gwamnatin Bala Mohammed ta jihar Bauchi ta yi alhinin rasuwar sarkin Ningi, Yunusa Muhammad Nayaya. Gwamna ya mika ta'azziyya.
Abun Bakin Ciki
Samu kari