Abuja
Shugaban alkalan Najeriya, Mai Shari'a, Olukayode Ariwoola ya shirya rantsar da sababbin alkalan Babbar Kotun Tarayya guda 12 a ranar Laraba 10 ga watan Yulin 2024.
Rahotanni sun bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake zama shugaban kungiyar ECOWAS karo na biyu a babban taron kungiyar na 65 da ya gudana a Abuja.
Fitaccen lauya a Najeriya Inibehe Effiong ya yi magana kan yarjejeniyar Samoa inda ya ce akwai lauje cikin nadi game da tsare-tsaren da suke ciki.
Sanata Shehu Sani yayi kira ga Shugaba Tinubu da ya hanzarta janye yarjejeniyar Samoa saboda cike take da sharuddan shaidanci. Yace har sauran shugabannin Afrika.
An kaddamar da wasu gidajen man CNG da kamfanin NNPC ya gina a Abuja, a wani bangare na gidajen man CNG 12 da aka kaddamar a lokaci daya a Legas da Abujan.
Majalisar dattawa tace za ta titsiye 'yan kwangila 39 da suka karba kudin gwamnati amma suka gaza zuwa su fara ayyuka. Za ta sa EFCC ta karbo kudin da suka kalmashe.
Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta fallasa wadanda ke da hannu a zanga-zanga da aka shirya kan ayyukanta a kasar nan.
Gwamnatin tarayya ta musanta yunƙurin halasta auren jinsi da ake zarginta da yi ta hanyar sa hannu a yarjejeniyar Samoa. Tace dokarta ta haramci tana nan daram.
Bola Tinubu ya rantsar da majalisar tattalin arzikin shugaban kasa (PECC) wadda ta kunshi jami'an gwamnati, 'yan kasuwa da mashawarta ciki har da Aliko Dangote.
Abuja
Samu kari