Bola Tinubu
Wasu manyan lauyoyi sun tofa albarkacin bakinsu kan matakin da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya dauka na sanya dokar ta baci a jihar Rivers mai arzikin mai.
Shugaban majalisar Rivers, Martin Amaewhule, ya goyi bayan matakin Bola Tinubu a jihar inda ya ce Gwamna Siminalayi Fubara ya karya dokoki da dama.
Hadimin tsohon shugaban kasa, Reuben Abati ya bayyana fatan majalisar kasar nan za ta iya tsige Bola Ahmed Tinubu daga kujerarsa saboda karya dokar kasa.
Mutanen yankin Neja Delta sun gargadi Bola Tinubu kan dokar ta baci da ya sanya a jihar Rivers da dakatar da gwamna Siminalayi Fubara da 'yan majalisar Rivers.
Kungiyar lauyoyin Najeriya, NBA ta yi Allah-wadai da cire Gwamna Fubara da ‘yan majalisa, tana mai cewa dokar ta-baci ba ta bai wa Shugaban Kasa wannan iko ba.
Jam'iyyar adawa ta PDP ta bayyana gwamnatin Bola Ahmed Tinubu da cewa ta na kokarin tabbatar da mulkin danniya da murde 'yan adawa da ke fadin kasar nan.
Sanata Shehu Sani ya sha rubdugu da ya goyi bayan dakatar da gwamna Siminalayi Fubara. Shehu Sani ya ce sanya dokar ta baci a Rivers ce mafita kawai.
Bayan ayyana dokar ya ɓaci, dakarun sojojin Najeriya sun mamaye fadar gwamnatin jihar Ribas, har an fara yaɗa jita-jitar ba a san inda Fubara ya shiga ya buya ba.
Kungiyar gwamnonin jam'iyyar PDP sun nuna rashin jin dadinsu kan dakatarwar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi wa Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers.
Bola Tinubu
Samu kari