Mafi karancin albashi
Gwamnan jihar Plateau ya amince da sabon mafi karancin albashi ga ma'aikatan jihar. Caleb Mutfwang ya amince a fara biyan ma'aikata sabon albashin N70,000.
Gwamnatin jihar Zamfara karkashin jagorancin Gwamna Dauda Lawal ta bayyana cewa nan ba da jimawa ba za ta fara biyan sabon mafi karancin albashi na N70,000.
Shugabannin ƙungiyar kwadago sun soki jihohin da ke jan kafa kan albashin N70,000, suna ganin hakan take hakkin ma’aikata ne a wannan mawuyacin lokaci.
Gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas, ya amince da sabon mafi karancin albashi ga ma'aikatan jihar. Gwamnan zai fara biyan sabon albashin daga watan Nuwamba.
Fasto Umo Eno, gwamnan jihar Akwa Ibom ya ba da tabbacin cewa zai biya ma’aikatan jihar albashi biyu a watan Disamba domin inganta bukukuwan Kirsimeti.
Kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC) ta shirya fara yajin aiki a jihohin da ba su fara biyan sabon mafi karancin albashi ba. Ta ba gwamnonin jihohin wa'adi.
Wasu gwamnoni a jihohin Najeriya har yanzu ba su fara biyan ma'aikata sabon mafi karancin albashi ba. Jihohin sun hada Zamfara, Taraba da Sokoto.
Gwamnatin jihar Borno ta fara biyan malaman makarantun firamare sabon mafi karancin albashi na N70,000. Malaman makarantan sun nuna farin cikinsu kan hakan.
Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ya amince da sabon mafi karancin albashi ga ma'aikatan jihar. Gwamnan ya amince zai biya ma'aikata albashin N80,000.
Mafi karancin albashi
Samu kari