Sojojin Amurka sun kai farmaki tekun Pacific sun kashe mutane 4. Sojojin sun zargi wani jirgin ruwa da safarar makamai. Ministan tsaro ne ya ba da umarnin kai harin.
Sojojin Amurka sun kai farmaki tekun Pacific sun kashe mutane 4. Sojojin sun zargi wani jirgin ruwa da safarar makamai. Ministan tsaro ne ya ba da umarnin kai harin.
Ministan harkokin wajen Najeriya, Yusuf Tuggar ya ziyarci Ibrahim Traore na kasar Burkina Faso. An saki sojojin saman Najeriya 11 da aka rike a kasar da jirginsu.
Karamin Ministan Tsaro a Najeriya, Dr. Bello Matawalle, ya musanta zargin alaka da yan ta’adda, yana kalubalantar masu zargi su kai shi kotu da hujjoji.
Gwamnan jihar Bayelsa, Sanata Duoye Diri, ya kadu kan mutuwar mataimakinsa. Gwamnan ya umarci a gudanar da bincike kan gawar bayan fara yada jita-jita.
Kotu a Akwa Ibom ta yankewa mutane hudu hukuncin kisa kan garkuwa da tsohon ma’aikacin ExxonMobil da yanke masa hannu bayan karbar kudin fansa N5m.
Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar hallaka wani tantitin jagoran 'yan bindiga a jihar Sokoto. Sojojin sun kashe jagoran 'yan bindigan ne yayin artabu.
Kungiyar Equipping The Persecuted ta yi gargadi kan yiwuwar hare-haren Kirsimeti a Arewa, DSS ta tabbatar da daukar matakan kariya yayin da ake shakku kan zargin.
Yakubu Gowon ya halarci taro a fadar shugaban kasa Abuja yayin da ake yada jita-jitar mutuwarsa a shoshiyal midiya, abin da ya karyata labarin da ba a tabbatar ba.
Gobara ta lalata gidaje huɗu a Asokoro, Abuja, a wani gini da ake alakanta da tsohon gwamnan Zamfara, Ahmed Yerima. Ana zargin farantan solar ne suka jawo gobarar.
Gwamnatin jihar Bauchi ta amince da karin albashi mai tsoka ga likitoci da ma'aikatan lafiya a fadin jihar. Ta amince da karin ne domin bunkasa ayyukansu.
Gwamnatin tarayya ta bude shirin YouthCred wanda aka samar domin bai wa matasa masu aikin yi bashin kudi, an kaddamar da shirin ga kowane matashi.
Labarai
Samu kari