Bankin FCMB Ya Samu Lambar Yabo daga DBN kan Bunkasa Kananan Sana'o'i a Najeriya

Bankin FCMB Ya Samu Lambar Yabo daga DBN kan Bunkasa Kananan Sana'o'i a Najeriya

Bankin First City Monument Bank (FCMB), ya samu lambar yabo sakamakom yadda yake tallafawa ƙananann sana'o'i (MSME), su bunƙasa da samun ci gaba a Najeriya.

A taron 2024 na Bankin Ci Gaban Najeriya (DBN) da aka gudanar a Legas, FCMB ya samu lambar yabo guda biyu.

An karrama bankin FCMB
Bankin DBN ya karrama bankin FCMB Hoto: @MyFCMB
Asali: UGC

An karrama shi kan tasirinsa wajen bai wa ƙananan sana’o’i bashi, da kuma bayar da gudunmawa wajen samar da ayyukan ci gaba.

A farkon shekarar 2024, FCMB ya bai wa ƙananan sana’o’i daban-daban bashin sama da Naira biliyan 180.

Wannan ya nuna jajircewar bankin wajen taimaka wa ƙananan sana’o’i da kuma gudunmawarsa ga ƙoƙarin ɗorewa muhalli a Najeriya.

Manajan-Daraktan Bankin, Hajiya Yemisi Edun, ta gode wa hukumar kan wannan lambar yabo da ta ba su.

Ta bayyana cewa bankin zai ci gaba da jajircewa wajen tallafa wa ƙananan sana’o’i domin su taka muhimmiyar rawa wajen inganta tattalin arziƙin Najeriya.

Ta kuma ƙara da cewa bankin na da burin samar da alaƙa tsakanin mutane, kuɗi da kasuwanni a faɗin Afirka.

A cewar Hukumar Kula da Kididdiga ta Ƙasa, ƙananan sana’o’i suna bayar da gudunmawar kashi 48 na kuɗaɗen shiga a Najeriya.

A gefe guda, bankin ya ce wannan ya yi daidai da manufarsa ta bunƙasa tattalin arziƙin ƙasa.

Bankin ya kuma samu tallafin dala miliyan 280 daga Cibiyoyin Kuɗi na Ci Gaba (DFIs), a 2023 domin tallafa wa ƙananan sana’o’i, musamman na mata, da kuma ayyukan makamashi.

Tsarin ‘Quick-Loans’ na bankin, wata hanyar sadarwa ce, wadda ke sauƙaƙa wa ’yan kasuwa samun bashi, inda dubban mutane suke samun bashi kowane wata.

Daga watan Janairu zuwa Yunin, 2024, tsarin ya samar wa masu ƙananun sana’o’i biliyoyin Naira domin bunƙasa kasuwancinsu.

Taron na DBN wanda ke gudana duk shekara, na zaɓar bankunan da suka yi bajinta wajen tallafa wa ƙananan sana’o’i.

A taron na bana an yaba wa FCMB bisa jagorancinsa a ɓangaren bayar da bashi don samun ci gaba mai ɗorewa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Legit.ng Branded Content avatar

Legit.ng Branded Content (marketing page) This account is used for publishing branded/sponsored content. For any enquiries please email: ads@corp.legit.ng or call: +234 810 304 48 99