Tara Naira Biliyan 110.9: Bankin FCMB Ya Kawo Sabuwar Damar Zuba Jari Mai Karfi
Legas - Rukunin kamfanonin FCMB da ke kan gaba a harkar hada-hadar kudi a Najeriya, ya gudanar da wani taro a kasuwar canjin kudi ta Najeriya (NGX) a shirinsa na tara jarin N110.9bn.
Taron ya yi tsokaci kan nasarorin da kamfanin ya samu a harkar kudi da kuma yin bayani kan dalilin da ya sa yake ba da damar saka hannun jari.
A ranar 29 ga watan Yulin 2024 FCMB ya sanar da da cewa ya bude kofa ga jama'a su sayi hannun jari a kamfaninsa da ya kai Naira biliyan 15.197 a kan N7.30 a kan duk guda daya.
Idan har aka saye hannayen jarin guda biliyan 15.197, kamfanin FCMB zai tara kimanin N110.9bn, wanda kuma za a rufe sayen hannun jarin a ranar 4 ga Satumbar 2024.
Kamfanin FCMB ya sanar da cewa ya na ci gaba da samu gwaggwabar riba, wadda ke nuna kwarewa, yin aiki tukuru da kuma sanin makamar aiki a kasuwar hada hadar kudi.
Nasarorin da FCMB ke ci gaba da samu alama ce da ke nuna cewa shugabannninsa sun san kan aiki, kuma suna da hangen nesa, kamar yadda ya yi bayani a taronsa a ofishin NGX.
Babban jami’in gudanarwa na rukunin FCMB, Mista Ladi Balogun, ya ce ba jama’a damar sayen hannun jari na daga cikin shirin bankin na biyan bukatun babban bankin Najeriya CBN.
Mista Ladi Balogun, ya kara da cewa, baya ga haka, kamfanin ya dauki wani tsari da zai samar da karin jari har na N397bn domin tafiyar da tsare-tsarensa na daban.
Shugaban rukunin FCMB ya kara da cewa:
"FCMB na ci gaba da tumbatsa, inda ta ke samun sababbin abokan hulda kusan miliyan biyu a duk shekara, kuma mun yi imanin cewa za mu ci gaba da haɓaka.
"A harkar banki, muna kusan na bakwai a mallakar kadarori kuma muna sahun farko a jerin manyan bankuna masu kula da harkar fansho (PFA) a kasar nan.
"Manufarmu ita ce mu ci gaba da bunkasa kudaden shiga ga masu zuba jarin kuma kudaden da za a samu daga wannan babban jarin zai haifar da ci gaban kasuwanci.
"Za mu mayar da hankali kan bayar da lamuni ga muhimman sassa kamar su noma, 'yan kasuwa, fannin fitar da kaya waje, wanda dai zai bunkasa tattalin arzikin kasar nan."
Mista Balogun ya jaddada cewa jarin zai baiwa FCMB damar bunkasa matsayinsa na kasuwa, saka hannun jari a sabbin fasahohi, da kuma ci gaba da samar da kima ga masu ruwa da tsaki.
Muhimman bayanai da aka tattauna a wajen taron sun haɗa da:
Riba mai ƙarfi: Kamfanin FCMB ya nuna habakar da ya ke samu na kudaden shiga da riba na shekara-shekara, wanda ke nuna nau'in kasuwancinsa na musamman da kuma aiwatar da dabaru masu inganci.
Tsare-tsare na faɗaɗa ayyukansa: Jarin da za a tara zai tallafawa bankin a sanya jari a manyan fasahohi na zamani, faɗaɗa kasuwancinsa, da kuma ƙarfafa matsayinsa a kasuwar banki.
Nasarori ta dalilin aiki tukuru: Duk da rashin tabbas na tattalin arziƙi, kamfanin FCMB ya ci gaba da samun nasarori, tare da tabbatar da jajurcewarsa na gudanar da aiki duk runtsi domin cimma nasara ta dogon lokaci.
Kwarewar gudanarwa: Tawagar shugabannin FCMB ta kunshi kwararru a masana'antar hada hadar kudi wadanda suka ajiye tarihi, wanda hakan ke ƙarfafa guiwar masu saka hannun jari kan da dora yakini a kamfanin.
Taron na FBO ya yi cikakken bayani game da manufofin kamfanin FCMB, haska kamfanin a matsayin wata dama ta saka hannun jari da zai samar da gwaggwabar riba.
Ta hanyar mayar da hankali kan samun ci gaba da kuma riba, kamfanin FCMB zai tsaya tsayin daka wajen ganin an yi amfani da jarin ta hanyar da zai samar da riba da dorewar kasuwanci.
Ana ƙarfafa masu saka hannun jari da su zuba jarinsu a rukunin kamfanonin FCMB domin habakar kuɗi da kuma kyakkyawan yakinin dorewar riba da ci gaban kasuwanci.
Asali: Legit.ng