Minista Pantami Ya Sallami Isma'il Adewusi, Ya Nada Bulus Shugaban NIPOST

Minista Pantami Ya Sallami Isma'il Adewusi, Ya Nada Bulus Shugaban NIPOST

  • Bayan sama da shekaru 30 a hukumar NIPOST, Barista Bulus Yakubu ya zama shugaba
  • Hukumar NIPOST na da hakkin sufurin kaya da lura da sakoni daga ciki da wajen Najeriya
  • Kwanakin bayan Minista Pantami ya samar da wani sabon tsarin zamanantar da hukumar

Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, ya nada Barista Bulus Yakubu matsayin mukaddashi shugaban hukumar akwatin sako, NIPOST.

Wannna ya biyo bayan sallamar Dr. Ismail Adebayo Adewusi daga kujerar.

Wannan na kunshe cikin jawabin da Diraktan yada labaran hukumar NIPOST, Mr Franklyn Alao, a ranar Alhamis a Abuja, rahoton DailyTrust.

Pantami
Minista Pantami Ya Sallami Isma'il Adewusi, Ya Nada Bulus Shugaban NIPOST
Asali: Twitter

Bulus ya karanci aikin Lauya a jami'ar Ahmadu Bello, daga bisani ya fara aiki a hukumar a 1990.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Barista Bulus dan asalin karamar hukumar Takum ne a jihar Taraba.

Gabanin sabon nadin nan da akayi masa, ya kasance sakataren kwamitin shugabannin NIPOST kuma wakilin hukumar ga majalisa.

Isa Ali Pantami Ya Yi Zarra Kan Sauran Ministoci, Gwamnati Ta Ba shi Lambar Yabo

Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani na kasa, Isa Ali Ibrahim Pantami ya samu lambar yabo a dalilin irin kokarin da yake yi a Najeriya.

Rahoton VON ya tabbatar da cewa Ministan ya samu kyautar “Best Performing Digital Minister for the Year 2022.” watau gwarzon Ministan zamani na 2022.

Wannan kyauta tana nufin a cikin Ministocin kasar, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami ne ya yi zarra a bangaren harkokin fasahar zamani a shekarar bana.

Asali: Legit.ng

Online view pixel