Matar Gwamna Fayosen tayi kyan kai
Uwargidan gwamna Ayo Fayose na jihar Ekiti, Feyisetan Fayose tafaranta ma wasu mata dake shirin haihuwa da marasa lafiya a asibitocin jihar.
Uwargida Feyisetan ta zagaya asibitocin jihar da dama inda ta biya ma wasu marasa lafiya kudaden asibiti da suka gagara biya, sa’annan ta raba kayan haihuwa ga mata masu juna biyu.
Wadanda suka amfana da wannan halin karamcin sun fito ne daga karamar hukumar Ekiti ta gabas, Gboyin, Emure; Ise/Orun da Ekiti na yamma, kuma sun taru ne a asibiti na musamman dake Ikere, inda suka gana da Uwargidan gwamna Fayose.
KU KARANTA: Ben Bruce ya roki a kawo ma Najeriya tallafin makara
Uwargida Feyisetan ta gudanar da wannan karamcin ne don murnan cikar gwamna Fayose shekaru 2 akan karagar mulki, tare da bikin cikar jihar Ekiti shekaru 20 da kirkira.
Uwargida Feyisetan ta biya ma masu juna biyu dake kan gwiwa a babban asibitin koyarwa na jami’a jihar Ekiti (EKSUTH) , da na asibitin kula da yara na Oke Iyimin, da na Ile Abiye kudaden asibiti. Daga nan sai ta bukaci al’ummar jihar dasu dinga zuwa asibiti akai akai ana duba lafiyarsu, don gane cututtukan dake damunsu a kan kari.
Ga sauran hotunan
Asali: Legit.ng