Yan Najeriya fiye miliyan 50 basu da aiki - NUT
Biyo bayan matsalar tattalin arziki da kasar nan take fuskanta, shugaban kungiyar malamai ta kasa (NUT) kwamared Michael Olukoya ya bayyana cewa sama da yan Najeriya miliyan 50 ne basu da aikin yi.
Olukoya yace ba’a taba samun matsalar tattalin arziki kamar wannan ba a shekaru 29 da suka wuce, inda ya bayyana matsalar ta shafi harkar ilimi sosai da sosai, sakamakon malamai basa samun albashi.
Shugaban yayi wannan jawabi ne bikin ranar malamai ta duniya daya gidana a garin Asaba jihar Delta, inda ya samu wakilcin shugaban kungiya na jihar kwamared Jonathan jemirieyigbe, Olukoya yace gwamnatocin jihohi sunyi amfani da wannan matsalar suka daina biyan albashin malamai, sa’annan ya nuna damuwarsa da yawan tantance malamai da ake yi a makarantu. Yace malamai na bin bashin albashi na watanni bakwai a yawancin jihohin kasar nan, wanda yace hakan na kashe ma malamai kwarin gwiwa.
KU KARANTA: An gano motar Dino Melaye jabu ce
Olukoya ya koka kan yadda ake wulakanta aikin malanta, inda yace ana tauye ma malamai hakkin su, wanda hakan ke rage musu kima a idon al’umma. A cewarsa malanta shi ne abinda kowace kasa tafi bukata, sai dai kash! Harkar ce tafi samun koma baya a Najeriya, sakamakon riokon sakainar kasha da mahukunta keyi mata.
Daga nan sai yayi kira ga gwamnatin tarayya data tabbatar da ganin cewa kwararrun malamai kadai ta dauka aiki a shirinta na daukan malamai 500,000 da ta keyi don samar da kwarewa da kuma gudanar da aiki yadda ya kamata.
Daga karshe Olukoya ya bukaci gwamnati da kada tayi kasa a gwiwa a yakin da take yi da kungiyar Boko haram, tare da gina makarantu musamman a yankin Arewa maso gabas day akin ya shafa.
Asali: Legit.ng