Matar Tinubu ta sha yabo

Matar Tinubu ta sha yabo

- Gwamna Akinwunmi Ambode ya jinjinnawa Sanata Remi Tinubu mai wakiltar mazabar Lagos ta tsakiya a majalisar dattijai a bisa yunkurinta

- Sanatar ta nemi daga likkafar jihar a kasar baki dayanta ta shawara a daukaka matsayinta a hukumanace da kuma ba ta tallafin kudi na musamman daga gwamnatin tarayyya

Matar Tinubu ta sha yabo
Sanata Remi da minjinta Ahmed Bola Tinubu

Gwamnatin jihar Lagos ta yabawa kudurin Sanata Oluremi Tinubu matar tsohon jihar, kuma shugaban Jam’iyyar APC,  a bisa matsin lambarta a majalisar na ganin jihar ta samu wani matsayi na musamman a hukumance da kuma ba ta tallafi na musamman.

A wata sanarawa da gwamnatin jiharta fitar wacce kuma kwamishinan yada labarai, Mista Steve Ayorinde ya sa hannu, ta ce, tarihin jihar Lagos ba zai manta da yunkurin Sanata Remi ba, na hangen nesa da kuma kokarinta na majalisar ta ba jihar wannan babban matsayi na cibiyar kasuwanci na Najeriya a hukumance, kuma birni ma fi samarwa gwamnatin tarayya kudin shiga.

KU KARANTA KUMA: Wani mai gida ya hallaka dan haya a Lagos

Sanarwar ta kuma ambato gwamnan jihar Akinwumi Ambode na cewa, ba karan tsaye ne ga shawarar majalisar na ajiye kudurin ba, yunkurin Santar, da kuma matsin lambarta, na da matukar muhimmanci, kuma zai kasance wani madubi na tattaunawa a duk inda aka soma maganar tattalin arzikin Najeriya.

Gwamnan ya kara da cewa, “yunkurin ya jan hankali ga  yadda za a tallafawa jihar a hukumance, ta yadda ita kuma za ta taimakawa miliyoyin ‘yan Najeriya…”

Sanarwar ta cigaba da cewa, duk da ajiye batun da majalisar ta yi a ranar Laraba, gaskiyar magana ita ce, jihar Lagos ta zama kadaura wata babbar inuwa kuma matattar ‘yan Najeria wajen nema da kuma samun arziki a daidaikunsu, da kuma jihohinsu na asali da kuma kasar baki daya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng