JAMB ta bayyana jami’o’in da suka fi shahara a Najeriya

JAMB ta bayyana jami’o’in da suka fi shahara a Najeriya

Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandari (JAMB) ta mayar da martanin cewa ba wai tana dogara da ra’ayin dalibai bane wajen gane makarantun da suke so.

JAMB ta bayyana jami’o’in da suka fi shahara a Najeriya
dalibai yayin zana jarabawar JAMB

Jaridar Economic Confidential ta bayyana jami’ar Ilori a matsayin wadda tafi samun yawan dalibai da suka nuna sha’awar shiga jami’ar, da suka kai 103,238 (Maza 51,082 da Mata 52,156). Wannan rahoton da jaridar ta buga ya nuna abubuwa dake janyo ra’ayin dalibai har suyi sha’awar jami’a sun hada da shaharar jami’a, rashin zuwa yajin aiki, saukin kudi, ababen more rayuwa da ingancin malamai.

Jami’i mai magana da yawun JAMB Fabian Benjamin yayin da yake ma jaridar Premium Times bayani a ranar 4 ga watan Oktoba yace “JAMB bata da wata hanyar gano wadannan alkalumma daga takardun da dalibai ke cikawa na nuna sha’awar shiga makarantu.

“Sai dai, abinda mukeyi duk shekara shi ne, muna gane makarantar da tafi samun yawan dalibai da suka nuna sha’awar shiga wata makaranta. Tun daga yan shekarun baya zuwa yanzu, jami’ar jihar Ilori ita ke kan gaba, wannan ba shi ke nuna itace jami’ar da tafi inganci ba. Wannan na nuni ne kawai ga abinda dalibai ke sha’awa.”

Jami’ar Ilori bata shiga yajin aikin kungiyar malaman jami’o’i na kasa, wanda wannan shine matsalar data addabi sauran jami’o’in kasar nan.Bugu da kari, zangon karatu na farawada karewa a kan lokaci a jami’ar Ilori.

KU KARANTA: Sojoji sun diran ma wani kauyen Neja Delta

Sai dai a wani bincike da jaridar Times Higher Education tayi na jerin makarantun da suka fi inganci a duniya, ta bayyana jami’ar Ibadan a matsayin jami’a daya tilo daga Najeriya da ta shiga jerin jami’u 801. Ana amfani da ingancin karantarwa, yawan gudanar da bincike, da kuma yadda ake kallon makarantar wajen shigar da makaranta cikin wannan jerin. Amma duk da haka, jami’ar Ilori ta sha gaban ta Ibadan wajen yawan dalibai masu sha’awar shigarta.

amma dangane da wadannan shikashikai da jaridar Economic Confidential ta fitar a baya, Benjamin yace babu yadda za’a hukumar JAMB ta san dalilin dake sa dalibai zabar wata makaranta fiye da wata

Jaridar ta bayyana jami’ar Ilori, jami’ar Benin, Jami’ar Ahmadu Bello, Jami’ar Nsukka da Jami’ar Bayero ta Kano a matsayin makarantun da suka fi shahara a cikin makarantu mallakar gwamnati n tarayya shekarar 2016.

Sai kuma jami’o’in jihar Nasarawa, Imo, Kaduna, Delta da jami’ar Adekunle Ajasin a matsayin wadanda suka fi shahara a tsakanin makarantu mallakan gwamnatin jihohin kasar nan. inda jaridar ta bayyana jami’ar Covenant, Afe Babalola, Babcock, Igbinedion da Bowen a matsayin wadanda suka fi shahara a cikin makarantu masu zaman kansu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel