Wani mutum ya kona hannun dan matarsa kan satar N200
- Ba dadewa aka ci zalin wani yaro dan shekara 8 a hannun mijin mamar shi saboda satar N200
- Rashin tausayin mutane sai kara karuwa yake yi, kamar yadda ake samun karin rohoton ni na cin zali da cin mutuncin kananan yara
Kamar yadda wani wanda ke amfani da dandalin sadarwa na Facebook ya bayyana a fusace mai suna Nwogu Davina yace wanda wani mutum ya ma wani yaron matar shi mai shekara 8 mummunan hukunci, wanda yake zargin sa da satar mai kudi N200.
Ga abunda ya rubuta a kasa:-
Yaron mai suna Sofeme, dane na farko ga Mrs Juliet wanda ta haifa a waje kafin aurenta da Mr Victor George wanda yake zaune a gida mai lamba 26, titin Owhor Rumudolo, sabon layi a Jahar Rivers, yaron yace shi dan Degema ne a jahar Rivers kuma shekarar shi 8.
Yaron ya tabbatar mana cewa yana rayuwa hannun mahaifiyarsa da mijinta rayuwa mai cutarwa da muzgunawa, da kyar suke cida shi da kyau, kuma baya zuwa makaranta.
A satin da ya gabata, yayin da yunwa ta fara galabar tar da karamin yaron, sai ya dauki kudin mijin mamar shi N200 dan ya saya GALA yaci, sai mijin mamar shi ya kona hannun shi da risho a matsayin hukuncin abunda yayi.
Dan haka yaron nan yana son a fidda mai hakkin sa, yan uwa mutanen Najeriya kuzo mu taimaka ma yaron nan kan zalunci da cuta da cin amana da aka mai, ban san yaron ba, amma wannan abun tausayi ne.
Asali: Legit.ng