Wata yarinya taga katuwar machijiya sai tayi mata wannan abu

Wata yarinya taga katuwar machijiya sai tayi mata wannan abu

- Wata karamar yarinya ta kama wasa da machijiyar data tsinta da wani hoto mai kyawun kallo

- Wacce irin katuwar machijiya ce zaki iya dauka a matsayinki na karamar yarinya?

Iyayen ta ne suka zaba mata wannan katuwar machijiyar? Abun da wannan yarinyar takeyi da wannan katuwar halittar zaiyi matukar baka mamaki.

Wata yarinya taga katuwar machijiya sai tayi mata wannan abu

Yarinyar tana wasa da macijiyar ta

Abin mamakine, ace yar karamar yarinya mai kimanin shekaru 3 da haihuwa ace wai tana wasa da katuwar machijiya. Tana matukar sonta kuma sun shaku da junan su, amman sai dai machijiyar tanada tsawon mita 3!

Waishi menene wa'annan iyayen suke tunani? Irin wannan machijiyar tana iya zama hatsari, ga kadan daga ciki misalin irin wa'annan manyan machizan.

Shekarun da suka wuce ne, wata katuwar machijiya mai tsawon mita 4, ta samu sa'ar shiga dakin kwanar wasu yara ta kashe yara guda biyu bayan ta kakkarya su, daya daga cikin yaran data kashe shekarar sa 5, a inda dayan kuma yakeda shekara 7. Inda machijiyar ta balle wata mahada ta gudu ta cikin silif. Sai daga baya yan sanda sukayi nasarar gano ta.

Saboda haka manyan machizai suna da saukin kashe kananan yara ta hanyar yamutsasu tare da kakkarya jikin su, duk da cewar suna da sha'awar ajiyesu a matsayin abin wasan su, wa'annan abin halittun sun zamo abin hatsari.

Wannan yar yarinyar nan dake cikin hoton nan tana sumbatar machijiyar nata haka kuma tana rungumanta a wasu lokuta. Muna fatar labarin nasu zai kare da kyau.

Yarinyar bata fahimci hatsarin tarayya da irin wa'annan manyan machizan ba. Yarinya ce yar karama kuma babu ruwanta domin kuwa tana matukar kyaunar abin wasan nata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng